ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Uwargidan Shugaban Ƙasa Ta Ƙaddamar Da Muhimman Ayyukan Ci Gaba A Jihar Jigawa

by Bello Hamza
2 months ago
Uwargidan

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Hadejia ta Jihar Jigawa, waɗanda suka da haɗa Cibiyar Fasaha ta Bola Ahmed Tinubu da Asibitin Wankin Ƙoda, Tituna da kuma Rumbum Tanada Abinci, domin bunƙasa ilimin fasahar zamani, ƙarfafa ayyukan kiwon lafiya, inganta hanyoyi da kuma tabbatar da wadatar abinci,daidai da manufar Shugaban Ƙasa ta Renewed Hope Agenda.

Cibiyar Fasaha ta Bola Ahmed Tinubu, wadda Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA) ta samar, za ta kasance cikakkiyar cibiyar ƙirƙire-ƙirƙire da fasahar zamani. Cibiyar ta ƙunshi ɗakin bincike na zamani (FabLab) don nazarin basirar AI, na’urorin mutum-mutumi (Robotics) da fasahar kiwon lafiya, tare da cibiyar ƙirƙire-ƙirƙire mai amfani da AI da kuma haɓaka kamfanoni masu tasowa (Startup Incubation Centre). Har ila yau, an tanadi ɗakunan jarabawar kwamfuta (CBT), wuraren aiki na haɗin gwiwa, babban zauren taro na zamani da kuma masaukin ɗalibai mai ɗaukar mutane 60.

Uwargidan Shugaban Ƙasar ta kuma ƙaddamar da Asibitin Sanata Oluremi Tinubu da Cibiyar Wankin Koda, wanda aka gina domin girmama ta, kuma gidauniyar FutureMap Foundation tare da eHealth Africa suka gina tare da cikakken kayan aikin likitanci na zamani, ciki har da na’urorin gwaje-gwaje da wankin ƙoda, domin faɗaɗa samun ingantaccen kiwon lafiya ga al’ummomin da ba su samun da isasshiyar kulawa.

ADVERTISEMENT

Domin tabbatar da ci gaba da samar da ingantattun ayyukan lafiya, asibitin ya haɗa da ɗakunan gwaje-gwaje na zamani, cibiyar wankin ƙoda, dakin tiyata da kuma sashen kula da mata masu juna biyu da haihuwa. Haka kuma, an tanadi tsarin samar da iskar shaka (oɗygen) na zamani, yayin da cibiyar ke amfani da makamashi mai sabuntawa domin tabbatar da cewa babu katsewar ayyukan lafiya.

Da take jawabi yayin ƙaddamarwar, Uwargidan Shugaban Ƙasar ta buƙaci matasa da su yi amfani da damar da cibiyar ke bayarwa domin ba da gudummawa wajen sauya fasalin tattalin arzikin Najeriya ta hanyar fasahar zamani. Ta kuma yaba wa Darakta Janar na NITDA, Kashifu Inuwa Abdullahi, CCIE, bisa jajircewarsa wajen tabbatar da cewa al’ummomi a faɗin asar nan suna cin moriyar fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Ƙaddamarwar ta kasance wani ɓangare na ziyarar farko da Uwargidan Shugaban Ƙasar ta kai Jihar Jigawa, inda ta kuma ƙaddamar da Shirin Rumbum Abinci na Ƙasa na Yankin Arewa maso Yamma, tare da buɗe wasu muhimman ayyukan more rayuwa, ciki har da Titin Bola Ahmed da Titin Oluremi Tinubu, wanda hakan ke ƙara nuna jajircewar gwamnatin Renewed Hope wajen faɗaɗa damar samun fasahar zamani, ingantaccen kiwon lafiya da ci gaban ƙasa mai haɗa kowa da kowa.

Uwargidan
Bello Hamza
+ postsBio
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Jihar Kano Za Ta Amfana Matuka Da Gidauniyar Aliko Dangote – Masu Ruwa Da Tsaki
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    An Nuna Damuwa Kan Sake Kamun Da DSS Ta Yi Wa Boɗejo Bayan Samun Belin EFCC
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Dole Al’ummar Arewa Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani —Alfa Musa
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina

MASU ALAKA

Labarai

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu
Labarai

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Next Post
Yadda Ayyukan Titunan Gwamnan Kaduna Suka Farfaɗo Da Ilimi Da Kiwon Lafiya Da Noma A Sabon Gari

Yadda Ayyukan Titunan Gwamnan Kaduna Suka Farfaɗo Da Ilimi Da Kiwon Lafiya Da Noma A Sabon Gari

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.