Rundunar Ƴansandan Jihar Osun ta ƙaddamar da bincike kan zargin kai hari ga jami’an Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a Ƙaramar Hukumar Odo-Otin, inda wasu da ake zargin ƴan daba ne suka kwashe katunan zaɓe na dindindin (PVCs).
Mai magana da yawun rundunar, DSP Abiodun Ojelabi, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa wasu jami’an INEC da ke rarraba katunan zaɓe na dindindin (PVCs) a Makarantar Firamare ta Oyinlola DC, Ward 2, Ƙaramar Hukumar Odo-Otin, wasu ƴan daba ɗauke da makamai kimanin goma sun kai musu hari.
Ya ce: “An ruwaito cewa ƴan dabar sun yi ta harbe-harbe sama ba ƙaƙƙautawa tare da kwashe fakitin PVC guda uku.”Ojelabi ya ce Kwamishinan Ƴansandan jihar, Ibrahim Gotan, ya yi Allah-wadai da lamarin tare da bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike domin ganowa, kamawa da gurfanar da waɗanda suka aikata laifin.
Mai magana da yawun rundunar ya buƙaci jama’a da su kwantar da hankula, su kasance masu bin doka, sannan su guji duk wani mataki da zai iya ƙara haddasa rashin zaman lafiya.
Ojelabi ya kuma roƙi mazauna yankin da waɗanda suka ga abin da ya faru kuma suke da sahihan bayanai da za su taimaka wajen binciken da ake gudanarwa, da su kai rahoto cikin gaggawa zuwa ofishin ƴansanda mafi kusa ko kuma su tuntuɓi rundunar ta lambobin gaggawa.
Adedayo Oketola, babban sakataren yaɗa labarai (CPS) na shugaban INEC, Joash Amupitan, ya shaida wa TheCable cewa binciken farko ya nuna cewa an sace wasu na’urorin Bimodal Ɓoter Accreditation System (BVAS) yayin lamarin.
Oketola ya ce: “Ƴansanda sun riga sun fara bincike kan wannan batu, don haka muna jiran sakamakon binciken. Ina ganin sun fara farautar waɗannan mutanen, kuma tabbas sun yi alƙawarin kama su.”Oketola ya ƙara da cewa satar kayayyakin ba za ta kawo cikas ko lalata tsarin zaɓen ba.Za a gudanar da zaɓen Gwamnan Jihar Osun a ranar 15 ga Agusta, 2026.














