ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, October 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƴansanda Sun Bankaɗo Kayan Wutar Lantarki Da Aka Sace A Kebbi

by Abubakar Sulaiman
2 months ago

Rundunar ƴansanda ta Jihar Kebbi ta samu nasarar gano ɗimbin kayayyakin wutar lantarki da wasu ɓata-gari suka sace a Ƙaramar Hukumar Bunza.

Mai magana da yawun rundunar, SP Bashir Usman, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, ya bayyana cewa an ƙwato waɗannan kayayyakin ne a ranar 25 ga watan Agusta a lokacin wani sumame da jami’ansu suka kai a yankin Kara da ke cikin garin na Bunza.

A cewar SP Usman, rundunar ta ƙaddamar da wannan sumame ne biyo bayan ƙorafe-ƙorafe da kuma fargabar da ake da ita kan yawaitar sace-sace da ɓata kayayyakin wutar lantarki a yankin. Ya bayyana cewa wannan dabi’a ta ɓarnatar da kayan amfanin gwamnati ta jefa al’ummomi da dama cikin duhu tare da katse musu wutar lantarki.

ADVERTISEMENT

Sanarwar ta tabbatar da cewa, a yayin sumamen, jami’an ‘yansandan sun samu nasarar ƙwato damin wayoyin wutar lantarki (cables) guda 10 da kuma wasu buhuna bakwai maƙare da irin waɗannan wayoyin daga hannun ɓata-garin.

Rundunar ‘yansandan ta kuma tabbatar da kama wani wanda ake zargi mai suna Mustapha Abubakar dangane da satar, inda ta ce tuni har an gurfanar da shi a gaban kuliya. SP Usman ya ƙara da cewa wannan nasara na nuni da aniyar rundunar na ganin ta daƙile ayyukan ɗaiɗaikun mutane da kuma ƙungiyoyin ɓata-gari da suka sa a gaba satar kayan amfanin al’umma.

LABARAI MASU NASABA

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Kamar yadda sanarwar ta nuna, Kwamishinan ‘Yansandan Jihar, Umar M. Hadejia, ya sake nanata ƙudurinsu na kare kayayyakin gwamnati da tabbatar da cewa duk wanda aka kama ya fuskanci hukunci daidai da doka, tare da yin kira ga mazauna yankin da su riƙa kai rahoton duk wani motsi da ba su yarda da shi ba.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh
  • Abubakar Sulaiman
    Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC
  • Abubakar Sulaiman
    Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’
  • Abubakar Sulaiman
    Aikin Titin Jirgin Ƙasa Na Kaduna Zuwa Kano Ya Kai Kashi 90%

MASU ALAKA

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya
Labarai

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

October 23, 2026
Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara
Manyan Labarai

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya
Ra'ayi Riga

Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

October 23, 2026
Next Post
2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya

Shugabar Jaridar LEADERSHIP Ta Halarci Bikin Aza Harsashin Cibiyar Ƙirƙire-Ƙirƙire Tare Da Remi Tinubu A Abuja

October 23, 2026
Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

October 23, 2026
An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

October 23, 2026
Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

October 23, 2026
Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

October 23, 2026
Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

October 23, 2026
Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina

Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.