ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ɓatan Dabon Naira Tiriliyan 210 A NNPCL: Kyari, Ajia da Wunti Sun Shirya Bayar Da Shaida

by Sulaiman
4 months ago
NNPCL

• Kwamitin Majalisar Dattawa ya bai wa Ojulari wa’adin ranar 13 ga Mayu

Tsohon Babban Daraktan Gudanarwa na Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL), Mele Kyari, ya bayyana shirinsa na bayar da shaida a binciken da Kwamitin Majalisar Dattawa kan Asusun Jama’a ke yi kan zargin bacewar Naira tiriliyan 210 daga asusun kamfanin.

Kwamitin, wanda Sanata Aliyu Wadada ke jagoranta, na binciken rahotannin tantance kuɗaɗen kamfanin mai na shekarun 2017 zuwa 2023.

ADVERTISEMENT

Kwamitin ya ce har yanzu bai samu gamsassun bayanai daga mahukuntan NNPCL ba kan abin da ya faru da Naira tiriliyan 210 ɗin.Kwamitin Wadada ya sha gayyatar shugaban kamfanin na yanzu, Bayo Ojulari, tare da yin barazanar bayar da umarnin kama shi in yaki amsa gayyatarsu, amma hakan bai haifar da sakamako ba.

Makonni biyu da suka gabata, kwamitin ya sake gayyatar Ojulari tare da umarnin ya zo da Kyari da wasu tsoffin manyan jami’ai biyu — Babban Jami’in Kuɗi, Umar Ajia, da Babban Jami’in Zuba Jari na kayayyakin mai da aka kammala sarrafawa (Upstream), Bala Wunti — zuwa zaman kwamitin na ranar Laraba.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Yayin da Ojulari bai halarta ba a ranar Laraba, Ajia ya halarci zaman inda ya rantse cewa zai bayar da shaida a zama na gaba.

Shi kuwa Kyari, duk da cewa bai halarci zaman ba, amma ya tuntubi Wadada yayin zaman domin tabbatar da cewa shi ma zai bayar da shaida a zama na gaba.

Wani mamba na kwamitin, Sanata Abdul Ningi, shima ya shaida wa takwarorinsa cewa, Wunti ya kira shi yana neman a ƙara masa lokaci domin ya samu damar amsa gayyatar a zama na gaba.

Sanatocin sun nuna rashin jin daɗinsu kan yadda Ojulari ke ci gaba da bayar da uzuri kan rashin halartar zaman kwamitin.

A ƙarshe, kwamitin ya bai wa Ojulari wa’adin zuwa ranar 13 ga Mayu domin ya bayyana gaban kwamitin ko kuma ya fuskanci yiwuwar kama shi bisa umarnin Majalisar Dattawa.

NNPCL
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
Next Post
Sojoji

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 18 A Yobe

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.