Ɗan takarar gwamnan Jihar Bauchi na Jam’iyyar NDC a zaɓen 2027, Barista Ibrahim Muhammad Kashim, ya fice daga jam’iyyar.
Kashim ya sanar da ficewarsa ne cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 16 ga watan Oktoba, 2026, wadda ya aike wa shugaban NDC na Ƙaramar Hukumar Bauchi.
Ya kuma aike da kwafin wasiƙar ga jaridar LEADERSHIP Hausa a ranar Litinin.
A cikin wasiƙar, Kashim ya ce ya yanke shawarar barin jam’iyyar ne bayan yin nazari mai zurfi, bisa dalilai na kansa.
Ya bayyana cewa murabus ɗin nasa zai fara aiki daga ranar da ya rubuta wasiƙar.
Kashim ya kuma gode wa shugabannin jam’iyyar da mambobinta bisa damar da suka ba shi ta yin aiki tare da su a cikin NDC.
Haka kuma, ya buƙaci shugabannin jam’iyyar su amince da murabus ɗinsa tare da sabunta bayanan da suka shafe shi domin nuna cewa ba ya cikin mambobinta.
Kashim ya taɓa riƙe muƙamin Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi (SSG) a lokacin gwamnatin Gwamna Bala Mohammed.
Ya kuma kasance cikin ’yan takarar gwamnan Bauchi 15 da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta saka a cikin jerin sunayen ’yan takarar zaɓen 2027 a jihar.
A baya, LEADERSHIP Hausa ta ruwaito cewa NDC ta zaɓi Ibrahim Muhammad Kashim a matsayin ɗan takararta na gwamnan Bauchi, yayin da Tata Alhaji ya kasance mataimakinsa domin shiga zaɓen 2027.














