Jam’iyyar APC ta sha alwashin kare ayyukan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta hanyar gabatar da hujjoji da bayanan ci gaban da aka samu, yayin da take shirin tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya bayar da wannan tabbaci ne a ranar Laraba, yayin jawabinsa na maraba a wajen ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Ya ce jam’iyyar za ta gabatar da nasarorin da ta samu, kuma za ta yi bayanin manufofinta, tare da amincewa da ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta, yayin da za ta bayyana dalilan da suka sa za a sake zaɓen Tinubu.
A cewarsa, gwamnatin ta aiwatar da manyan sauye-sauyen tattalin arziki da nufin magance matsalolin da suka daɗe suna addabar tsarin tattalin arzikin ƙasar, tare da shimfiɗa tubalin samun ci gaba mai ɗorewa.
Yilwatda ya ce wajibi ne jam’iyyar ta yi wa ’yan Nijeriya bayani kan manufofin waɗannan sauye-sauye, ci gaban da aka samu zuwa yanzu da kuma sauran ayyukan da ake buƙatar kammalawa.
Ya kuma jaddada muhimmancin bunƙasa ababen more rayuwa, ciki har da hanyoyi, ayyukan samar da wutar lantarki, ayyukan iskar gas, layukan dogo, tashoshin jiragen ruwa, ababen more rayuwa na noma da kuma hanyoyin sadarwa na zamani.
Ya ce waɗannan na daga cikin muhimman fannoni da jam’iyyar ya kamata ta yi wa ’yan Nijeriya bayani a kansu gabanin zaɓen 2027













