A yau Laraba 14 ga watan Oktoba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da wasikar taya murnar bude bikin baje kolin harkokin ciniki a birnin Guangzhou na kasar Sin wato Canton Fair karo na 140 na Sin.
Xi ya nuna cewa, tun kaddamar da bikin yau shekaru 70 da suka wuce, ya taka muhimmiyar rawa wajen ingiza harkokin cinikayya tsakanin Sin da kasashen waje, kuma ya zama dandali mai amfani na Sin wajen fadada bude kofarta ga ketare bisa babban mataki, da ingiza gina dandalin tattalin arzikin duniya mai bude kofa.
A cikin sabon yanayi, Sin na fatan hada hannu da kasashen duniya, don kare tsarin cinikayya tsakanin bangarori da yawa, da kuma tabbatar da kwanciyar hankali ga tsarin samar da kayayyaki, kana da fadada damar hadin gwiwar cinikayya ta kasa da kasa mai amfanawa kowa.
Ban da wannan kuma, da ingiza dunkulewar tattalin arzikin duniya dake hade kowa da kowa, da ci gaba da karfafa kuzari da ingancin wadatar duniya.
A yau ne aka bude bikin Canton Fair karo na 140 a birnin Guangzhou na lardin Guangdong. (Amina Xu)













