Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, bai halarci bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta kasa ta farko da za ta jagoranci babban zaben 2027 ba, wanda aka gudanar a ranar Talata.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, wanda shi ne dan takarar jam’iyyar APC mai mulki, ya samu wakilcin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume.
Sai dai Atiku Abubakar bai samu wakilci a wajen taron ba. Kokarin jin dalilin rashin halartarsa bai yi nasara ba, domin mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba. Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, bai kuma mayar da martani ga sakonnin da aka aika masa ba kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Sai dai Sakataren Yada Labarai na Kasa na jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ya shaida wa Daily Trust cewa jam’iyyar ta samu wakilcin Babban Lauyanta na Kasa, Farfesa Osumbor, a wajen taron.
Kwamitin Zaman Lafiya na Kasa (NPC), tare da hadin gwiwar Cibiyar Kukah, ne suka shirya bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar.
Yarjejeniyar na da nufin tabbatar da cewa jam’iyyun siyasa, ’yan takarar shugaban kasa da magoya bayansu sun himmatu wajen gudanar da yakin neman zabe cikin lumana, mutunta hukumomin zabe da kuma mayar da hankali kan manufofi da batutuwan da suka shafi al’umma gabanin babban zaben 2027.
Da yake jawabi a wajen bikin rattaba hannun, Shugaban NPC, Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya), ya yi kira ga jam’iyyun siyasa, ’yan takara da masu magana da yawun yakin neman zabe da su gudanar da harkokinsu cikin ladabi, mutunci da kuma girmama juna.














