ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kano Ta Ware Naira Biliyan 996.3 Ga Ayyuka 1,557 A Cikin Shekaru Uku

by Sulaiman
3 weeks ago
Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta ware jimillar Naira biliyan 996.29 domin aiwatar da ayyuka 1,557 a kananan hukumomi 44 na jihar cikin kusan shekaru uku na mulkin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Kwamishinan kula da saye da kwangiloli na gwamnati, sa ido da tantance ayyuka, Nura Ma’aji Sumaila, ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin wani taron manema labarai na kasa da kasa kan yadda ake aiwatar da ayyukan, rarraba su a fadin jihar, bin ka’idojin sayen gwamnati da kuma yadda ake tafiyar da kudaden ayyukan.

Sumaila ya ce an kammala ayyuka 867, wadanda suka kai kashi 55.68 cikin 100 na jimillar ayyukan, yayin da ayyuka 654, wato kashi 42 cikin 100, ke ci gaba da gudana. Ya kara da cewa ayyuka 26 suna matakin bayar da kwangila, yayin da wasu 10 ke shirin samun kwangila.

ADVERTISEMENT

A cewarsa, an samu takardar ‘Certificate of No Objection (NOC)’ kan kwangilolin da kudinsu ya kai Naira biliyan 695.20, yayin da aka tantance takardun biyan kudade na ayyukan da suka kai Naira biliyan 444.75.Ya ce amincewar NOC ta wakilci kashi 69.78 cikin 100 na jimillar kudin kwangilolin, yayin da kudaden da aka tantance suka kai kashi 44.64 cikin 100.

Kwamishinan ya bayyana cewa ayyuka 598 da kudinsu ya kai Naira biliyan 299.36 suna cikin kananan hukumomin birnin Kano guda takwas, yayin da ayyuka 653 da suka kai Naira biliyan 287.90 suke a kananan hukumomin wajen gari 36.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ya ce akwai wasu ayyuka 37 na hadin gwiwa da suka kai Naira biliyan 159.50, wadanda suka shafi kananan hukumomi da dama, yayin da ayyuka 269 na fadin jihar da sauran ayyuka suka kai Naira biliyan 249.54.

Sumaila ya bayyana cewa ayyukan da suka shafi kananan hukumomi da dama sun hada da fadada hanyoyi, gina gadoji, samar da fitilun tituna masu amfani da hasken rana, tsarin kula da zirga-zirgar ababen hawa da kuma hanyoyin da suka hada kananan hukumomi daban-daban. Ya gargadi cewa bai kamata a danganta irin wadannan ayyuka da wata karamar hukuma guda ba, domin kauce wa kirga aiki daya sau biyu.

Daga cikin manyan ayyukan da ya ambata akwai aikin gidaje masu yawa na Rijiyar Gwangwan da ke Dawakin Kudu, wanda kudinsa ya kai Naira biliyan 113.19; fadada titin Katsina kan Naira biliyan 24.77; aikin samar da kayayyakin more rayuwa na biranen zamani na Naira biliyan 21.90; hanyar Madobi-Yako-Kafin Maiyaki/Kiru mai darajar Naira biliyan 27.74; da kuma aikin gidaje na Rural Model City wanda kudinsa ya kai Naira biliyan 22.

Sai dai ya ce wasu manyan ayyuka masu tsadar gaske, ciki har da aikin gidajen Dawakin Kudu da na Rural Model City, har yanzu suna matakin bayar da kwangila ne saboda ana jiran kammala matakan da suka dace na bin ka’idojin bayar da kwangiloli.

Sumaila ya tabbatar wa al’ummar jihar da abokan huldar cewa, ma’aikatar za ta ci gaba da sa ido kan tsarin sayen gwamnati, tantance takardun biyan kudade da kuma duba ayyuka, domin tabbatar da cewa an samu cikakkiyar fa’ida da darajar kudaden da aka kashe.

Kano
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
Next Post
Kamfani A Kano Ya Miƙa Wa KCPC Kayayyaki Na ₦28.6m Da Amincinsu Ke Dab Da Ƙarewa

Kamfani A Kano Ya Miƙa Wa KCPC Kayayyaki Na ₦28.6m Da Amincinsu Ke Dab Da Ƙarewa

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.