Da safiyar yau Jumma’a, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta Sin ya gudanar da taron manema labarai, inda ya gabatar da bayanai game da yadda ake share fagen bikin kasuwancin aikin ba da hidimomi na duniya na 2026 wato CIFTIS, tare da amsa tambayoyin ‘yan jarida.
A taron, an bayyana cewa, a yayin bikin bana, kusan kasashe 90 da kungiyoyin kasa da kasa za su shirya baje koli da tarurruka, kuma kamfanoni sama da 1800 za su shiga cikin baje kolin. A lokacin da ake bude dandamalin baje kolin da cinikin ingatattun ayyukan ba da hidimomi na kasa da kasa da taimaka musu wajen fadada shiga kasuwannin Sin, har ila yau a karon farko, an kafa wani yanki na musamman na “fitar da aikin ba da hidimomin Sin zuwa ketare” a wannan bikin, don tallafa wa kamfanonin Sin wajen fadada samun kasuwa a duniya a bangaren ba da hidima, da kuma habaka karin “ingatattun ba da hidimomin Sin” wajen shiga kasuwar duniya.
A yayin taron, an bayyana cewa, a bana bikin CIFTIS zai kara mai da hankali kan fifikon kirkire-kirkire da cinikin ba da hidimomi, inda za a baje kolin sabbin fasahohi da tsare-tsare da sakamako a fannoni kamar sadarwa da kiwon lafiya mai aiki da kimiya da fasaha, kana da ilimi mai aiki da tsarin fasaha da kuma kare muhalli da sauransu. Kamfanoni da cibiyoyi sama da 90 za su gabatar da sakamakon bincike, kuma karo na farko a duniya, za a samar da mabambantan fasahohi da kayayyaki da hidimomi masu aiki da kirkire-kirkiren zamani, da kuma baje kolinsu a kasar Sin.Za a gudanar da bikin CIFTIS a wannan karo a birnin Beijing daga ranar 9 zuwa 13 ga watan Satumba dake tafe. (Amina Xu)














