Akalla mutane uku sun rasu, yayin da wasu da dama suka samu raunuka sakamakon turmutsitsi da ya afku a Gidan Gwamnatin Jihar Neja da ke Minna.
Daily Trust ta bayyana cewa, Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a daren Talata, bayan wasu matasa da ake zargin suna shirin gudanar da zanga-zanga kan mutuwar wasu ma’aikatan hakar ma’adinai 37 da suka rasu a baya-bayan nan, an gayyace su zuwa Gidan Gwamnatin domin dakile zanga-zangar.
Daga cikin wadanda suka rasu akwai wata mata mai suna Dije da ’yarta, Hurairat, wadanda suka kasance ’yan gudun hijira daga garin Allawa na Karamar Hukumar Shiroro.
An ce wasu mutane sun garzaya Gidan Gwamnatin ne bayan jita-jitar cewa Gwamna Mohammed Umaru Bago zai raba N10,000 ga wadanda suka hallara.
Wadanda suka samu raunuka suna karbar magani a Babban Asibitin Minna.
Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Bologi Ibrahim, ya ce gwamnatin jihar za ta fitar da sanarwa kan lamarin nan ba da jimawa ba.
Shi ma Kakakin Rundunar ’Yansandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce zai tabbatar da sahihancin rahoton kafin ya yi karin bayani.














