Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT), Nyesom Wike, ya ce Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya samu nasara a zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar kwanan nan ne saboda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da gudanar da sahihin zaɓe cikin ‘yanci da adalci.
Wike ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin da yake duba wuraren da ambaliyar ruwa ta shafa a wasu sassan Babban Birnin Tarayya Abuja.
Da yake magana kan zaɓen gwamnan Osun na ranar 15 ga Agusta, Wike ya yi watsi da zarge-zargen cewa gwamnatin tarayya ta yi amfani da ƙarfinta wajen karkatar da zaɓen, yana mai cewa Tinubu ya bar tsarin dimokuraɗiyya ya yi aiki yadda ya kamata.
A cewar Wike, sakamakon zaɓen ya nuna cewa gwamnatin tarayya ba ta yi amfani da ikonta wajen hana ‘yan adawa samun nasara ba.
Ya ce, “Shugaban ƙasa ya kira shi… ya taya shi murna (Adeleke). Me hakan ke nuna muku? Idan Tinubu bai bada damar gudanar da zaɓe cikin ‘yanci da adalci ba, da za su yi nasara ne? A’a!”
Wike ya kuma yi watsi da zargin cewa an yi amfani da abin da ake kira “ƙarfin gwamnatin tarayya” wajen tasiri kan sakamakon zaɓen, yana mai cewa irin waɗannan zarge-zarge ya kamata a tabbatar da su da hujjoji.














