A yau Litinin ne mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana cewa mahukuntan gwamnatin Lai Ching‑te, sun saba barnata dukiyar da al’ummar yankin Taiwan suka sha wahalar tarawa a ayyukan diflomasiyyar kudi. Ta wannan hanya, ‘yan siyasar Taiwan din na gudanar da cin hanci, da raba kyautuka, da juya akalar ra’ayoyi, da neman tasiri ta amfani da kudi don biyan bukatun ‘yan aware, masu rajin neman “’Yancin Taiwan”, da burikan siyasa na kashin kansu.
Ga kasashe irinsu Palau, kulla abun da suka kira “Huldar Diflomasiyya”, ba ya nufin cimma burikan kasa da al’umma, maimakon haka, wata dabara ce kawai ta cika aljifan wasu tsirarun mutane dake cin ribar hakan.
A cewar jaridar Solomon Star, yankin Taiwan ya kara yawan tallafin kudi da yake baiwa Palau, daga dalar Amurka miliyan 18 a shekarar da ta gabata zuwa dala miliyan 25 a bana, a wani mataki na saye zukatan ‘yan siyasar kasar, wadda tsibiri ce a yankin tekun Fasifik.
Kazalika, mahukuntan Taiwan sun mika kyautar kudi kai tsaye, har kusan dala 281,000 ga tsohon shugaban Palau, da manyan ‘yan siyasar kasar masu ci, da ma wasu daidaikun ‘yan majalisar dokokin kasar. (Saminu Alhassan)














