A gun taron manema labaru da ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar a yau Litinin, ma’aikatar ciniki ta kasar Sin ta bayyana cewa, za ta dauki matakai don sa kaimi ga raya ciniki ta yanar gizo da yin kirkire-kirkire a wannan fanni.
Ma’aikatar ta bayyana cewa, za a raya yankin gwaji na ciniki ta yanar gizo na kasar, da sa kaimi ga kirkire-kirkire kan raya tsarin ciniki ta yanar gizo, don bunkasa cinikin mai inganci bisa tsari mai kyau, da yanayin gudanar da ciniki mai nagarta, da kuma fadada kasuwar cinikin baki daya.
Kana za a gudanar da wasu ayyuka, don goyon bayan manufar kasar ta raya sansanin fitar da kayayyaki ta ciniki ta yanar gizo yadda ya kamata. (Zainab Zhang)














