ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, August 3, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Alamomin Fara Ruɓewar Hannu Bayan Ɗorin Gida

by Sani Anwar
2 months ago
Hannu

Ɗorin gida ko na gargajiya, na iya jawo mummunan lahani ga tsokoki, jijiyoyin jini, jijiyoyin laka, haɗi da shi kansa ƙashi. 

Hakan na faruwa ne, sakamakon katsewar gudanawar jini sakamakon ɗaurin ɗorin.

Lahani na fara faruwa ne daga awa uku zuwa shida bayan ɗaurin da ya katse gudanawar jini a gaba da ɗaurin.

ADVERTISEMENT

Idan katsewar jini ta zarce, za ta iya haifar da ruɓewar hannu ko ƙafa; wanda daga ƙarshe zai tilasta yanke sashin a asibiti ɗungurungum.

Amma akwai alamomi biyar da za su iya taimakawa wajen gano katsewar gudanawar jini ta faru, sannan kuma hannu ko ƙafa su fara ruɓewa.

LABARAI MASU NASABA

DSS Da ‘Yan Sa-kai Sun Kashe Fitaccen Jagoran ‘Yan Bindiga Da Mayaƙansa Sama Da 60 A Katsina

‘Yan Ta’adda Sun Kashe Sojoji Shida, Sun Sace Mutane 75 A Zamfara

Alamomin na fara bayyana ne, tun daga awanni ukun farko da suka haɗa da:

1- Matsanancin ciwo a inda aka yi ɗaurin karayar.

2- Shanyewar hannu ko ƙafa: A yayin da jijiyoyin laka suka samu lahani, hannu ko ƙafa za su shanye; wato rashin ƙwari zai bayyana, sannan mutum ya gaza motsa yatsun hannun nasa ko na ƙafarsa.

3- Gushewar ji a fata: Idan aka taɓa hannu ko ƙafar mutum, ba zai ji ba, ko kuma ya riƙa jin dindiris, sagewa, jin kamar shokin ko kuma kamar ana tsitstsira masa allura.

4- Koɗewa: Hannu ko ƙafa za su koɗe ko kuma su ɗashe, hakan na nuni ga ƙamfar jini a sashen.

5- Ɗaukewar bugawar zuciya: Akwai wasu sassa a jikin mutum da ake iya jin yadda zuciya ke bugo jini zuwa sassan jiki, wato ‘pulse’. A hannu, ana iya jin bugawar zuciya a kan gaɓar gwiwar hannu da kuma tsintsiyar hannu; daidai ƙasan babban yatsan hannu. Haka nan, ana iya jin ƙafa a kan tafin sawu. 

Da zarar waɗannan alamomi sun fara bayyana, sai a garzaya zuwa asibiti; domin ceto hannun ko ƙafa daga ruɓewa. Amma idan har aka yi buris da faruwar hakan, daga ƙarshe zai tilasta yanke hannun ko ƙafa a asibiti; wanda kuma yanke wani sashen jikin mutum, na nufin samun nakasa ne kai tsaye.

Hannu
Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Amfanin Ganyen Magarya Ga Lafiya Dan Adam
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Yadda Ciwon Hanta Ke Yaduwa Tsakanin Ma’aurauta
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Sake Daukar Shettima Da Tinubu Ya Yi Zai Kara Karfafa APC A Zaben 2027 –Farfesa Yerima
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Shugaban Rundunar Sojojin Nijeriya Ya Nemi Haɗin Kan Fararen Hula

MASU ALAKA

DSS
Manyan Labarai

DSS Da ‘Yan Sa-kai Sun Kashe Fitaccen Jagoran ‘Yan Bindiga Da Mayaƙansa Sama Da 60 A Katsina

August 3, 2026
Zamfara
Labarai

‘Yan Ta’adda Sun Kashe Sojoji Shida, Sun Sace Mutane 75 A Zamfara

August 3, 2026
Alkalin Babbar Kotun Kebbi Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci, Bayan Shafe Mako Guda A Hannun ‘Yan Bindiga
Manyan Labarai

Alkalin Babbar Kotun Kebbi Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci, Bayan Shafe Mako Guda A Hannun ‘Yan Bindiga

August 3, 2026
Next Post
CBN Ya Ƙara Wa’adin Ranar Fara Aiwatar Da Sabuwar Dokar Tsaro Ga Masu PoS

CBN Ya Ƙara Wa'adin Ranar Fara Aiwatar Da Sabuwar Dokar Tsaro Ga Masu PoS

LABARAI MASU NASABA

DSS

DSS Da ‘Yan Sa-kai Sun Kashe Fitaccen Jagoran ‘Yan Bindiga Da Mayaƙansa Sama Da 60 A Katsina

August 3, 2026
Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Fahimtar Juna Da Aka Cimma Tsakanin Amurka Da Iran

Iran Ta Musanta Iƙirarin Trump Kan Sabbin Tattaunawa da Amurka

August 3, 2026
Zamfara

‘Yan Ta’adda Sun Kashe Sojoji Shida, Sun Sace Mutane 75 A Zamfara

August 3, 2026
Alkalin Babbar Kotun Kebbi Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci, Bayan Shafe Mako Guda A Hannun ‘Yan Bindiga

Alkalin Babbar Kotun Kebbi Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci, Bayan Shafe Mako Guda A Hannun ‘Yan Bindiga

August 3, 2026
Kamfanin Abinci Na ‘BUA Foods’ Ya Samu Ribar ₦292.27bn A Rabin Farkon 2026

Kamfanin Abinci Na ‘BUA Foods’ Ya Samu Ribar ₦292.27bn A Rabin Farkon 2026

August 3, 2026
Hannu

WAFCON 2026: Ƴan Wasan Nijeriya 2 Ba Zasu Buga Wasan Ƙarshe Na Rukunin C Ba

August 2, 2026
Babban Bankin Sin: Za A Ci Gaba Da Gudanar Da Matakan Saukaka Harkokin Kudade

Babban Bankin Sin: Za A Ci Gaba Da Gudanar Da Matakan Saukaka Harkokin Kudade

August 2, 2026
Yawan Tikitin Kallon Fina Finan Sin Da Aka Sayar A 2026 Ya Zarce Yuan Biliyan 23

Yawan Tikitin Kallon Fina Finan Sin Da Aka Sayar A 2026 Ya Zarce Yuan Biliyan 23

August 2, 2026
Hannu

Sojoji Sun Daƙile Harin Ƴan Ta’adda, Sun Ceto Mutane 9 A Zamfara

August 2, 2026
Sin Ta Fitar Da Shirin Shekaru 5 Na Daukaka Tsarin Tallata Da Samar Da Kayayyaki Domin Kyautata Hidimomi A Kauyuka

Sin Ta Fitar Da Shirin Shekaru 5 Na Daukaka Tsarin Tallata Da Samar Da Kayayyaki Domin Kyautata Hidimomi A Kauyuka

August 2, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.