ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ban Sha Wata Wahala Ba A Gwagwarmayar Shiga Harkar Fim —Hadiza

by Rabi'at Sidi Bala
3 months ago
Fim

Kamar kowane mako, yau ma shafin Rumbun Nishadi na tafe da wata bakuwar ta musamman, daga cikin masana’antar shirya finafinan hausa ta Kannywood, wato HADIZA ADAMU MAINA wacce aka fi sani da HADIZA MAINA.inda ta bayyanawa masu karatu batutuwan da suka shafi sana’arta ta fim, da kuma rayuwarta.

Ga dai tattaunawar tare da wakiliyar Jaridar LEADERSHIP HAUSA RABI’AT SIDI BALA Kamar haka:

Da farko masu karatu za su so su ji cikakken sunanki tare da sunan da aka fi saninki da shi.

ADVERTISEMENT

Sunana Hadiza Adamu Maina, an fi sanina da Hadiza Maina.

Ko za ki fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

An haife ni a garin Kaduna, na yi firamare har zuwa jami’a. Bayan nan shi ne na tsinci kaina a chikin harkar fim na Kannywood.

Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma harkar fim?

Lokacin da nake ‘secondary school’, na yi ‘Hausa Dramatic Club’, wanda shi ne ya kara jan hankali na zuwa yin fim. Bayan nan kuma na hadu da wani ‘Producer’, wanda ya kara min karfin gwiwa don na shiga fim.

Za ki yi kamar shekara nawa da fara fim?

Ina da kimanin shekaru 20 da fara harkar fim, amma na daina bayan nayi aure, ban ci gaba ba sai shekara daya da ta wuce.

Ya gwagwarmayar shiga cikin masana’antar ta kasance?

Ban sha wata wahala ba.

Ya batun iyaye ko ‘yan’uwa lokacin da za ki sanar musu kina sha’awar fara fim, shin kin samu wani kalubale daga gare su?

Iyayena sun ba ni izini bayan da na fada masu ra’ayina na shiga harkar fim. Ban samu kalubale a wannan fannin ba.

Ya farkon farawar ta kasance?

Farkon farawata, ta  kasance tare da nasara.

Da su wa ki ka fara haduwa a farkon shigarki kannywood?

Na hadu da jarumai da dama irin su; Hamisu Lamido Iyentama, Adamu Zango da su Ishak Sidi Ishak, da dai sauransu.

Da wane fim ki ka fara?

Na fara da fim me suna ‘Dabaibayi’ sai ‘Shahada’

Daga lokacin da ki ka fara kawo yanzu, kin yi finafinai sun kai kamar guda nawa?

Na yi fim kimanin guda 45.

Ko za ki iya fadowa masu karatu kadan daga finafinan da ki ka fito ciki?

Dabaibayi, Watarana, Tahazir, Shahada, Gadan Zinare. A yanzu bayan dawowata kuma akwai kamar su; Manyan Mata, Kaddara, Saddika, Zabi Biyu, da dai sauran su.

Cikin finafinan da ki ka fito wanne ne ya zamo bakandamiyyarki, wanda ki ka fi so, kuma me ya sa?

Manyan Mata da Kuma Zabi Biyu.

Wane irin nasarori ki ka samu game da fim?

Alhamdulillah na samu nasarori da yawa da ‘Awards’ a lokacin da harkar fim kafin nayi aure, kuma har yandu ina ganin nasara a al’amuran.

Ko akwai wani kalubale da ki ka taba fuskanta sanadiyyar fim, ko cikin masana’antar?

Na fuskanci kalubale da dama, amma na yi godiya ga Allah da ya ban ikon wuce su.

Ko akwai wani fim wanda ki ka fito cikinsa, daga baya ki ka yi da-kin-sanin fitowa cikinsa?

Eh! Akwai wani fim din da na yi wanda ‘role’ din da na yi ba abun alfahari bane, amma sai Allah ya taimaka fim din ma bai fito ba.

Wane abu ne ya taba faruwa da ke na farinciki ko akasin haka wanda ba za ki taba iya mantawa da shi ba a rayuwa?

Akwai abubuwan farin ciki da dama da suka same ni kama daga kyaututtuka, da damammaki da sauransu.

Ya ki ka dauki fim a wajenki?

Na dauki fim sana’a, da kuma wurin da zan iya fadakar da al’umma.

Mene ne burinki na gaba game da fim?

Burina shi ne na yi fim na gama da kowa lafiya, a ta yadda ko na tafi ba za a manta da ni ba.

Ko kina da ubangida a masana’anyar Kannywood?

Ubangidana a Kannywood shi ne Alhaji Abdul-amat.

Bayan fim kina wata sana’ar ne?

Eh! Ina da sana’o’i da dama na hannu wanda nake yi bayan harkar fim.

Ya alakarki take da sauran jarumai, da kuma wadanda kuke tare da su tun kafin ki fara fim?

Gaskiya ina da alaka mai kyau tsakanina da jarumai da kowa.

Wasu na kokawa game da masana’antar kannywood, a takaice ya za ki yi wa masu karatu bayanin yadda masana’antar Kannywood take?

Kannywood ba kamar yadda mutane suke kallonta bane, kowacce irin masana’anta ko ba ta fim ba akwai batagari, kuma akwai na kwarai a cikinta, Kannywood ita ma kamar haka take, ba kowa da ka gani a cikinta bane yake kamar yadda wasu suke tunani.

Ko akwai wasu matsaloli a cikin masana’antar Kannywood wadanda ki ke ganin ya kamata a gyara su?

Akwai matsaloli da dama wanda ya kamata a gyara. Kamar matsalar mata wanda suke shigowa harkar fim amma sai su fada hannun batagari da sunnan za su basu daukaka.

Misali ki zama shugaba, wane irin cigaba ki ke ganin za ki kawo ga masana’antar Kannywood?

A gaskiya da akwai wasu abubuwa da dama mutum zai iya kokarin ya ga an canjasu In sha Allah a kannywood.

Wacce shawara za ki bawa masu kokarin shigowa cikin masana’antar Kannywood?

Su shigo tsakaninsu da Allah da kuma zuciya mai kyau, ba tare da kwadayin abun hannun wani ba.

Ko akwai wata shawara da za ki bawa sauran abokan sana’arki na fim?

Mu rike juna da amana, kuma mu tsarkake harkarmu.

Ko kina da wadanda za ki gaishe da su?

Ina gaishe da daukacin al’umma, da kuma abokan aikina gabadayansu.

Fim
Rabi'at Sidi Bala
+ postsBio
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Yadda Alaƙata Da Adamu Zango Ta Bunƙasa A Kannywood —Jarumi Ibrahim Sodangi 
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Fim Ko Gaske:Yaushe Masu Kallon Fina-finai Za Su Daina Daukar Fim A Matsayin Gaske
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Fim ɗin ƙaddara: Anya Ana Samun Irin Wannan ƙaddarar Kuwa?
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Ko Kafa Ƴansandan Jihohi Zai Taimaka Wajen Kawo Ƙarshen Matsalolin Tsaro?

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Matsalar Tsaro Da Tsadar Kayan Noma Na Barazana Ga Samar Da Abinci A Daminar Bana

Matsalar Tsaro Da Tsadar Kayan Noma Na Barazana Ga Samar Da Abinci A Daminar Bana

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.