ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ci-ma-zaunen Ƴan Siyasa Ne Ke Tunanin Yin Maguɗi A Zaɓen 2027 – Makarfi

by Yusuf Shuaibu
2 months ago
makarfi

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Ahmed Mohammed Makarfi, ya musanta iƙirarin cewa za a iya yin maguɗin zaɓen babban zaɓen 2027, yana mai cewa irin waɗannan kalamai halayen ƴan siyasa ne da ba sa son yin aikin wahala da ake buƙata don cin zaɓe.

A cikin wata hira da ƴan jarida, Makarfi ya ce ya kamata ƴan siyasa su mayar da hankali wajen samun magoyon baya da ƙarfafa tsarin jam’iyyunsu, da kare sahihancin tsarin zaɓe maimakon yin zargin cewa ana shirin yin maguɗi tun da wuri.

Da yake mayar da martani kan damuwar da ake nunawa a wasu sassa cewa zaɓen gaba zai iya samun matsala, tsohon gwamnan ya ce ƴan siyasar da ke yin hasashen maguɗin zaɓe tun kafin a fara kaɗa ƙuri’a kawai suna neman uzuri ne.

ADVERTISEMENT

“Kawai wannan tunanin mutum mai kasala ne, tun daga farko, zai ce za a yi maguɗin zaɓe a 2027.

“Me ya sa za ka tashi ka bar zaɓe? Ka yi aiki don ka ci zaɓe, ka yi aiki don ka hana maguɗi, amma me ya sa za ka riƙa cewa abubuwa ba za su yi daidai ba? A’a, abubuwa suna daidai, sai dai idan mu muka bari su zama ba daidai ba,” in ji Makarfi.

LABARAI MASU NASABA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

Makarfi ya yi wannan bayani ne a daidai lokacin da ake ƙara samun haɗakar siyasa gabanin zaɓen 2027, inda jam’iyyun adawa da masu ruwa da tsaki ke nuna damuwa kan yadda za a gudanar da zaɓen.

Tsohon shugaban kwamitin riƙo na jam’iyyar PDP ya bayyana cewa maimakon haifar da tsoro da rashin yarda a tsarin zaɓe, ya kamata jam’iyyun siyasa su mai da hankali kan tsayar da nagartattun ƴan takara da kuma shawo kan ƴan Nijeriya su mara musu baya.

Ya kuma jaddada cewa dimokiraɗiyya tana bunƙasa ne idan ƴan siyasa suna shiga zaɓe cikin tsari da gaskiya maimakon yin hasashe kan sakamakon tun kafin a fara yaƙin neman zaɓe.

Game da halin da PDP ke ciki, Makarfi ya nuna kwarin gwiwa cewa jam’iyyar na da karfin gaske duk da ƙalubalen da take fuskanta.

“Tabbas, daga cikin dukkan jam’iyyun siyasa, ina ganin PDP, saboda tana da tushe mai ƙarfi kuma ba ta dogara da mutum guda ba, tana da makoma mai kyau.”

Sai dai ya amince cewa jam’iyyar ta fuskanci matsaloli kuma mambobinta sun samu rarrabuwan wajen kaɗa ƙuri’a a zaɓen shugaban ƙasa na baya, abin da ya ce yana nuna gaskiyar siyasa ta lokacin.

A cewarsa, zaɓe yana shafar abubuwa da dama, ciki har da biyayya ga jam’iyya, ƙabila, addini, cancantar ɗan takara da kuma yanayin da ake ciki.

“Wasu mutane za su zaɓa ne saboda jam’iyya. Wasu saboda addini ko ƙabila. Wasu kuma kawai saboda ba sa son wani,” in ji shi.

Makarfi ya ce babu wani ɗan takara ko jam’iyya da ya kamata ya ɗauka cewa nasara ta tabbata tun kafin zaɓen 2027, yana mai gargaɗin cewa ƴan Nijeriya suna ƙara wayewa wajen zaɓar shugabanni.

“Waɗanda ke cikin takara suna da aiki mai yawa a gabansu. Duk wanda yake tunanin zai zauna kawai nasara ta riga ta tabbata, yana raina hankalin ƴan Nijeriya,” in ji shi.

Tsohon gwamnan ya kuma sake jaddada cewa dole ne jam’iyyun siyasa su bi dokokin zaɓe da ƙa’idoji yayin fafutukar siyasa, yana mai cewa mutunta doka na da matuƙar muhimmanci wajen ƙarfafa tsarin dimokiraɗiyyar Nijeriya.

makarfi
Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

MASU ALAKA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
Tambarin Dimokuradiyya

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

September 5, 2026
Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
Tambarin Dimokuradiyya

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

September 4, 2026
Ko INEC Na Da Hannu A Rikice-rikicen Jam’iyyun Siyasa A Nijeriya?
Tambarin Dimokuradiyya

INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027

August 28, 2026
Next Post
Fahimtar “Karin Damar Sin” Bisa Tsarin “Amfani Da Kirkire-Kirkire A Mabambantan Bangarori” Na Sin

Fahimtar "Karin Damar Sin" Bisa Tsarin "Amfani Da Kirkire-Kirkire A Mabambantan Bangarori" Na Sin

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.