Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF) ta sanar da cewa ta kai hare-haren sama kan wani sansanin da ake zargin ‘yan ta’adda ke amfani da shi a Yaganari, da ke yankin Gezuwa a Jihar Borno. Rundunar ta ce an gudanar da harin ne ta hannun Operation HAƊIN KAI (OPHK) bayan samun sahihan bayanan sirri kan sabbin motsin ‘yan ta’adda a yankin.
A cikin wata sanarwa da Kakakin NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar, ya ce an fara gudanar da ayyukan leƙen asiri da sa ido ta sama a ranar 10 ga Yuli, 2026, inda aka tabbatar da wanzuwar sansanonin ‘yan ta’adda da cibiyoyin adana kayayyakin aikinsu. Bayan tabbatar da bayanan, jiragen yaƙin rundunar suka kai jerin hare-hare kan wuraren.
NAF ta ce hare-haren sun lalata sansanonin da kayayyakin ‘yan ta’addan, tare da kashe da dama daga cikinsu. Rundunar ta bayyana cewa wannan nasara na ƙara nuna yadda ake ci gaba da takaita motsi da damar sake haɗuwa da ƙungiyoyin ‘yan ta’adda ta hanyar hare-haren sama da ake kai musu akai-akai.
Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Aneke, ya yabawa jami’an da suka gudanar da aikin bisa ƙwarewa da jajircewarsu. Ya kuma tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da haɗa kai da sojojin ƙasa wajen kai hare-hare kan duk wani sansanin ‘yan ta’adda a ko’ina suke, domin hana su samun mafaka ko damar sake farfaɗowa. Ya ƙara da cewa Rundunar Sojin Nijeriya na ci gaba da samun gagarumar nasara a yaƙin da take yi da ta’addanci a sassan ƙasar.














