ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rashin Tsaro Na Barazana Ga Zaben 2027 —Rahotanni

by Yusuf Shuaibu and Sulaiman
3 months ago
Tsaro

A cewar rahotanni, saura kusan watanni bakwai kacal a gudanar da zaben 2027, amma matsalar rashin tsaro na ƙara ƙamari wanda hakan Babbar barazana ne ga dimokuraɗiyyar Nijeriya.

Rahotanni daga kafafen yaɗa labarai, sun nuna cewa a tsakanin watan Janairu zuwa Mayu na shekarar 2026 kaɗai ƴan Nijeriya 5,272 aka kashe sakamakon rashin tsaro.

A cewar Rahoto na 15 kan tashin hankali a Nijeriya, wanda ‘Nijeriya Watch’ ta fitar kuma Dakta bitus Nwankwo Ukoji ya tsara, tare da goyon bayan Dakta Abiola bictoria Ayodokun, an kashe ƴan Nijeriya 222,137 a cikin lamuran tashin hankali 46,182 a jihohi 36 da Abuja tsakanin shekarar 2006 zuwa 2025.

ADVERTISEMENT

Yawan mutanen da suka mutu a shekarar 2026 ya ja hankalin hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da masu fafutukar kare haƙƙin Ɗan’adam da manyan lauyoyi wanda suka gargaɗi cewa za a iya gudanar da zaben da aka shirya ranar 16 ga Janairu da 6 ga Fabrairu, 2027, a cikin yanayin rashin tsaro da ba a taba ganin irinsa ba. Ci gaba da hare-haren ƴan ta’adda, barnar da ƴan daba ke yi, sace-sacen mutane da sauran laifukan tashin hankali a mafi yawan sassan ƙasar, musamman a yankin arewa maso gabas da arewa maso yamma da arewa ta tsakiya, wanda a yanzu abun ya shiga zuwa kudu maso yamma, wanda suka haifar da tashin hankali da tsoro a cikin al’umma.

A daidai lokacin da zaben 2027 ke ƙaratowa, ra’ayin da ke fitowa daga fannoni da dama na cewa, shugabancin INEC da manyan jami’an ƴansanda da ƙungiyoyin kare haƙƙin Ɗan’adam da kuma ƙungiyoyin farar hula, suna shakka kan cewa ba za a iya gudanar da zabe a Nijeriya a wannan lokacin cikin tsaro ba.

LABARAI MASU NASABA

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

Sai dai kuma manyan jam’iyyun adawa, kamar PDP da ADC da NDC, a makon da ya gabata, sun yi gargaɗi kan jinkirta zaben, suna cewa yin hakan zai zama kamar miƙa dimokuraɗiyyar ƙasa ga ƙungiyoyin ta’addanci.

Shugaban INEC, Farfesa Amupitan, ya yi gargaɗi sau biyu a kwanakin baya, kowanne lokaci yana jan hankali kan ɗaukar matakin gaggawa game da jadawalin zaben 2027.

Da farko, a lokacin ziyarar Babban Sufeton Ƴansanda, IGP, Olatunji Disu, Amupitan ya nemi goyon baya da haɗin kai daga ƴansandan Njeriya, kafin zaben da ke tafe.

A cikin wata sanarwa da daraktar yaɗa labara na hukumar, bictoria Eta-Messi, ta fitar ta ce, shugaban INEC ya bayyana cewa maguɗin zabe da sayan ƙuri’u, da barazanar tashin hankali na daga cikin abubuwan da ka iya rage amincewar jama’a da kuma kawo haɗari ga tsaron ƙasa.

Ya jaddada buƙatar ɗaukar matakan tsaro tun kafin lokacin zabe, ciki har da cikakken nazarin haɗarin, don gano wuraren da matsala ka iya tasowa da kuma aiwatar da dabarun rage haɗari a gaba, maimakon jiran matsala ta bullawa.

“Rashin tsaro a sassa daban-daban na ƙasar nan na barazana ga gudanar da sahihin zabe mai cike da gaskiya da adalci. Yana da muhimmanci mu gudanar da cikakken bincike kan haɗarin tsaro kafin zaben,” in ji Amupitan.

Ya kafa kwamitin tattaunawa na hada-hadar hukumar kan tsaron zabe, (ICCES), a matsayin ginshiƙin tsarin tsaro na zabubuka, yana bayyana shi a matsayin tsaron harkokin zabubuka.

A cewarsa, nasarar hukumar na dogara ne kan kwamitin ICCES gaba ɗaya.

Amupitan ya tabbatar da aniya INEC na aiki kafaɗa da kafaɗa da ƴansanda da sauran hukumomin tsaro don gudanar da zabe cikin lumana, mai cike da gaskiya da ke nuna ainihin ra’ayin mutanen Nijeriya.

Da yake mayar da jawabi, IGP Disu ya tabbatar wa hukumar cewa ƴansandan Nijeriya na samar da muhalli mai tsaro don zaben 2027, tare da alƙawari mai ƙarfi na cewa ba za a nuna bambanci ga kowa ko kowace jam’iyya ba.

Ya ce rundunar za ta cika ayyukanta da ƙwarewa, rashin nuna bambanci da kuma bin doka da tsarin mulki na 1999 da dokar zabe da sauran dokoki ya ɗora mata.

Disu ya bayyana cewa rundunar ta riga ta fara nazarin barazanar da dabaru da taswira na leƙen asiri a ƙasar baki ɗaya don gano wuraren tashin hankali da sabbin haɗarin tsaro tun kafin ranakun zabe.

Ya ƙara tabbatar wa INEC da cewa za a samu cikakken tsaro ga jami’an zabe da muhimman kayan aiki da cibiyoyin tattara sakamako da sauran muhimman kayan aikin zabe a duk tsawon tsarin.

Kwana kalilan baya, a taron lacca na shekara-shekara na ƙungiyar AANISS ta shirya, Amupitan ya koma kan batun, wannan karon, ya jawo hankali kan barazanar da ke tashi ga tsarin zaben Nijeriya.

Ya bayyana cewa Nijeriya na shiga wani mummunar yanayi bayan an fitar da jadawalin zaben 2027, inda ya lura cewa zabuka na shugaban ƙasa da ƴan majalisar ƙasa da aka tsara a ranar 16 ga Janairu, 2027, da kuma zabukan gwamnoni a 6 ga Fabrairu, 2027, yanzu ba kawai alamun siyasa ba ne, lamari ne na matsalar tsaro da ta kuno kai.

Amupitan ya gano abin da ya kira haɗakar barazana uku masu zurfi da ke fuskantar zaben Nijeriya, canjin yanayi a kafafen sada zumunta, yaɗa labaran bogi ta hanyar fasahar sadarwa da wurgar bayanai daga ƙasashen waje, duk sun ƙara kuno kai a daidai lokacin da zabe yake ƙara ƙaratowa a ƙasar nan.

“Ba tare da yanayi mai kyau ba, ƴancin mutane na yin zabe na cikin haɗari,” in ji shi.

A cewar rahoton na 15 kan tashin hankali a Nijeriya, wanda ‘Nigeria Watch’ ta saki kuma Dakta bitus Nwankwo Ukoji ya tattara tare da taimakon Dakta Abiola bictoria Ayodokun, adadin ƴan Nijeriya da aka kashe gaba ɗaya ya kai 222,137 a cikin abubuwan tashin hankali 46,182 a duk jihohi 36 da Abaja tsakanin 2006 zuwa 2025. Rahoton ya gano cewa ta’addanci, fashi a ƙauyuka, satar mutane, rikicin manoma da makiyaya da kuma ayyukan jami’an tsaro su ne manyan abubuwan da ke haddasa tashin hankali a faɗin ƙasar a 2025.

Jihohin da abin ya fi shafa a 2025.

Borno 2,221, Neja 1,438, Zamfara 1,426, Benuwai 811 da kuma Katsina 731.

Mafi tsoratarwa a cikin rahoton ‘Nigeria Watch’ shi ne halin barna a karkara. Mutuwar da aka danganta da farmakin ƴan bindiga ta ƙaru zuwa 3,974 a shekarar 2025, daga 1,452 a shekarar 2024, kusan sau uku cikin shekara guda, kuma idan wannan yanayin ya ci gaba, zai iya sanya babban matsin lamba kan tsaro musamman a lokacin zaben 2027.

Tarihin zaben Nijeriya yana ba da wani yanayi mai tayar da hankali ga damuwowi a yanzu. Musamman, a lokacin shirin zabuka, ana samun wani yanayin tashin hankali na kashe-kashen manyan ƴan siyasa wanda masana suke cewa ya kafa wani mummunan tarihi.

Yayin da Nijeriya ke gudanar da zabe a ranar 16 ga Janairu da 6 ga Fabrairu, 2027, watanni bakwai masu zuwa na iya yanke hukunci ba wai kawai wanda zai mulki Nijeriya daga 2027 ba, har ma ko ana iya amincewa da tsarin da ke yanke wannan hukunci ko a’a.

Tsaro
Yusuf Shuaibu
+ posts Bio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa
Tsaro
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Umarnin Kawo Karshen Matsalar Tsaro
Rahotonni

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

September 5, 2026
Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
Rahotonni

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

September 5, 2026
Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
Rahotonni

Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki

September 5, 2026
Next Post
Jarin Waje Ya Inganta Hada-hadar Zuba Jari A Kasar Sin

Jarin Waje Ya Inganta Hada-hadar Zuba Jari A Kasar Sin

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.