ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sautin Muryar Da Aka Fallasa Kan El-Rufai Ya Haifar Da Zazzafar Muhawara

by Yusuf Shuaibu
2 months ago
El-Rufai

Wani sautin murya da ake zargin na ɗan takarar gwamnan Jihar Kaduna ƙarƙashin jam’iyyar ADC, Alhaji Isa Ashiru, ya jawo cece-kuce tare da haifar da zazzafar muhawara a cikin jam’iyyar, inda masu goyon bayansa ke musunta cewa an ƙirƙiri sautin muryar ne kawai don a ɓata masa siyasa, yayin da magoya bayan tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ke tabbatar da biyayya gareshi.

An ruwaito cewa duk da cece-kucen da ake yi, matar El-Rufai, Aisha El-Rufai ta bayyana goyon bayanta ga ɗan takarar jam’iyyar ADC.

A cikin wani rubutu a shafin Facebook ɗinta da aka tabbatar, ta ce “Babu gudu ba ja da baya, babu miƙa wuya. Yin faɗa da gwagwarmaya ba ya hana mutuwa.

ADVERTISEMENT

“Sautin murya, wasiƙu, bidiyoyi duk abin da suke nunawa ko da Isa Ashiru zai yi mu’amala ba tare da Malam El-Rufai da iyalinsa. Na ce wa’adi ɗaya ne kawai, ba za a juyar ba, in Allah ya yarda,” ta rubuta.

An ce sautin muryar wadda aka yaɗa a kafafen sada zumunta, tana ɗauke da wani tattaunawar waya tsakanin Ashiru da wani dattijo daga kudancin Kaduna. A cikin muryar, ana zargin mai magana da ya yi watsi da El-Rufai, da ya kasance wani jigo a cikin jam’iyyar ADC.

LABARAI MASU NASABA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

Duk da haka, ba a tabbatar da sahihancin sautin muryar ba, kuma har yanzu ba a tabbatar ba ko muryar Ashiru ce ko kuma shi ne ya yi maganganun da aka danganta masa.

A cikin sautin muryar, an ce mai magana ya bayyana cewa ya shiga ADC ne domin wata dabara ta siyasa wadda ke nufin samun tikitin takarar gwamna a jam’iyyar.

“Mun je ADC ne kawai don samun tikitin takarar gwamna a cikin jam’iyya domin mu samu nasara a zaɓe. Saboda jam’iyyar PDP ta rabu zuwa gida biyu. Wike yana jagorantar wani ɓangare, yayin da Tanimu Turaki ke jagorantar ɗaya ɓangaren, kuma duka ɓangarorin suna kotu,” a cikin sautin muryar.

Mai magana ya ƙara da cewa haɗuwarsa da El-Rufai ta samo asali ne daga buƙatar siyasa ba daga ra’ayin kansa ba.

Mai magana ya kuma zargi cewa an jingine El-Rufai a siyasa a cikin jam’iyya, yana kwatanta halin da yake ciki a yanzu a matsayin sakamakon abubuwan da ya aikata a baya.

Yayin da ake martani a cikin sautin muryar, wani shahararren ɗan ADC a Kaduna ta arewa kuma abokin Ashiru, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda bai samu izinin yin magana kan batun ba, ya yi watsi da sautin muryar tare da bayyana cewa na bogi ne.

“Ba mu yarda cewa muryarsa ce ba. A wannan zamani na fasahar sadarwa komai zai yiwu. An yi haka ne kawai don yunƙurin ɓata sunan Ashiru a gaban jama’a,” in ji abokin Ashiru.

Majiyar ta zargi ƴan siyasa masu hamayya da shirya kamfen na sharri kan Ashiru a daidai lokacin da ake fafatawar siyasa don zaɓen 2027.

Wata majiya cewa fitowar sautin muryar abun mamaki ne, ta ƙara da cewa, masoya tsohon gwamna sun haɗu a ranar Lahadi don tattauna sakamakon sautin muryan da aka saki da kuma tabbatar wa ƴan jam’iyya da ci gaba da goyon bayansu ga El-Rufai.

“A matsayinmu na masu biyayya ga El-Rufai a cikin jam’iyyar ADC, mun haɗu a yau don tattauna batun da kuma bayyana biyayyarmu ga El-Rufai. Za mu yi duk mai yuwuwa don kare martabarsa a Jihar Kaduna,” in ji majiyar.

Kazalika, jigon jam’iyyar ya ƙi yin ƙarin bayani, yana mai cewa za a gudanar da wani taro nan ba da jimawa ba don tantance matsayin masu biyayya ga El-Rufai a cikin jam’iyyar ADC.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, Ashiru bai fitar da wata sanarwa a hukuma ba kan sautin muryar da aka yaɗa a kafafen sada zumunta.

An yi ƙoƙarin jin ta bakin Ashiru ta wayar salula amma abun ya ci tura, haka kuma bai amsa saƙonnin da aka tura masa ta WhatsApp ba.

A shekara ta 2015, Isa Ashiru ya ƙalubalanci El-Rufai a zaɓen fid da gwani na gwamnan jam’iyyar APC, amma ya sha kashi a hannun El-Rufai.

Bayan haka, ya koma jam’iyyar PDP, ya shiga zaɓen fid da gwani na jam’iyyar, ya kuma samu tikitin takarar gwamna a jam’iyyar. Ya kuma shan kashi a hannun El-Rufai.

A shekarar 2019, Ashiru ya samu tikitin takara a cikin jam’iyyar PDP kuma ya fafata da El-Rufai amma ya sha kaye a zaɓen. A shekarar 2023, ya sake fafatawa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP da Sanata Uba Sani a wani zaɓe mai tsauri, wanda shi ma ya sha kaye.

Yanzu ya koma jam’iyyar ADC kuma ya samu tikitin takarar gwamnan Jihar Kaduna na jam’iyyar karo na huɗu.

El-Rufai
Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

MASU ALAKA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
Tambarin Dimokuradiyya

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

September 5, 2026
Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
Tambarin Dimokuradiyya

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

September 4, 2026
Ko INEC Na Da Hannu A Rikice-rikicen Jam’iyyun Siyasa A Nijeriya?
Tambarin Dimokuradiyya

INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027

August 28, 2026
Next Post
Babban Jami’i: Nazartar Mahangar Xi Jinping Mabudi Ne Na Fahimtar Kasar Sin Ta Zamani

Babban Jami'i: Nazartar Mahangar Xi Jinping Mabudi Ne Na Fahimtar Kasar Sin Ta Zamani

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.