ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Samu Ruɗani Kan Rashin Bayyana Jerin Ƴan Takarar Jam’iyyun Siyasa Na Zaɓen 2027

by Yusuf Shuaibu
2 months ago
siyasa

Bayan wasu makonni da jam’iyyun APC da PDP da ADC da NDC da kuma LP suka kammala zaɓen fid da gwani, har yanzu jam’iyyun ba su fitar da jerin sunayen ƴan takara na ƙarshe ba, wanda hakan ke jawo damuwa kan makomar siyasar ƴan takarar.

Rahotanni sun bayyana cewa duk da sanarwar da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), ta yi kwanan nan cewa za ta ba dukkan jam’iyyun siyasa lambobin sirri na hukuma don amfani da adireshinta a ranar Jumma’a, 26 ga Yuni, 2026, wajen saka sunayen, sai dai makomar ƴan takara a zaɓukan fitar da gwani na jam’iyyun a baya-bayan nan ba sa da tabbas.

Yayin da jam’iyyun siyasa suka kammala zaɓen fitar da gwani a makonni da suka wuce, sun ƙi fitar da jerin sunayen ƴan takarar gwamnan jihohi da na ƴan majalisar tarayya da kuma na majalisar jihohi na zaɓen 2027.

ADVERTISEMENT

Rashin saka sunayen ya haifar da zarge-zargen siyasa mai yawa a cikin jam’iyyun.

An gano cewa jam’iyyun siyasa na ɓoye jerin sunayen ƴan takara ne da gangan don tabbatar da cewa lokacin da aka fitar da sunayen, zai zama tashin hankali ga ƴan takara da suka fusata don kai ƙara da ƙalubalantar tsarin da aka bi wajen zaɓen fitar da gwani.

LABARAI MASU NASABA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

A yayin da APC ta bayyana cewa jerin zai fito nan ba da jimawa ba, reshen PDP da ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Mista Nyesom Wike, yake jagoranta, shi ma ya shaida cewa suna jiran taron shugabannin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar don fitar da sunayen.

Sai dai da take kare matakinta na rashin fitar da sunayen ƴan takarar da suka yi nasara daga zaɓen fitar da gwani a fili, jam’iyyar NDC ta nace cewa babu wani doka da ke tilasta wa jam’iyyun siyasa yin hakan.

A nata ɓangaren, ADC ta ce har yanzu tana cikin bin jadawalin INEC da ƙa’idojin gabatar da sunayen ƴan takara. A gefe guda, LP ta ce ta amince da jerin sunayen kuma za ta fara loda su zuwa adireshin INEC a ranar 28 ga Yuni.

A cikin jam’iyyar APC, shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya nuna ƙaruwar samun fusata a tsakanin ƴan majalisa da suka faɗi zaɓen fitar da gwani.

Akpabio, yayin da yake magana a lokacin taron ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓe na ƙasa na jam’iyyar APC don zaɓen gwamnan Ekiti, ya buƙaci shugabannin jam’iyyar su kula da jerin sunayen ƴan takara na ƙarshe da hankali.

Ya ce wasu daga cikin abokan aikinsa a majalisar ƙasa sun fusata sakamakon zaɓe fitar da gwani.

“Jam’iyya ce mafi girma. Ni dai ina roƙon jam’iyyar kawai ta tabbatar cewa idan sun saki jerin sunaye na ƙarshe, su haɗa da mu duka. Wasu daga mutanena suna ta ƙorafi,” in ji shi.

A ɓangarenta, NDC ta yi iƙirarin cewa babu wani doka da ke tilasta wa jam’iyyun siyasa su bayyana jerin sunayensu. Yayin da yake magana da manema labarai, sakataren jam’iyyar na ƙasa, Mista Osa Director, ya yi watsi da suka kan yadda jam’iyyar ke tafiyar da tsarin zaɓen ƴan takara, yana mai jayayya cewa dokar da ke kula da zaɓen cikin jam’iyya ba ta wajabta a bayyane a sake sunayen ƴan takara da suka samu nasara.

Ya tsaya kan cewa ƴan takara da suka fafata a zaɓen sun riga sun samu bayani game da sakamakon, yayin da waɗanda ba su gamsu da sakamakon ba suna da ƴancin zuwa kotu.

“Dokar ba ta buƙatar bayyana sakamakon ga jama’a ba,” in ji shi.

Ya bayyana cewa NDC ta bi dukkan dokokin da suka wajaba, yana mai cewa INEC tuni tana da bayanan da suka dace daga zaɓen fitar da gwanin.

Mai magana da yawun NDC ya ƙara fayyace cewa ranar 26 ga Yuni da aka kayyade na bayanan ƴan takara ga hukumar zaɓe an yi shi ne don bai wa jam’iyyun siyasa damar lodawa da tabbatar da jerin sunayensu na ƙarshe.

Haka kuma a martaninsa kan batun, PDP mai goyan bayan Wike ta ce tana jiran taron shugabannin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar don amincewa da jerin dukkan ƴan takara.

A cewar sakataran harkokin yaɗa labarai na PDP, Haruna Jungudo, “Mun gudanar da dukkan ayyukan zaɓe na neman ɗan takara, ciki har da ƙorafe-ƙorafen waɗanda suka ji ba su da gaskiya a yadda aka gudanar da aikin.”

“Aikinmu a wannan ɓangaren, duka aikin zaɓen fitar da gwani da ƙarar da aka shigar daga baya, INEC ta sanya ido a kai.

“Yanzu muna jiran taron shugabannin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar wanda ake sa ran zai gudana nan ba da jimawa ba don tabbatar da aikin. Sai dai bayan taron shugabannin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar an tabbatar da shi ne kawai mu a matsayin jam’iyyar siyasa za mu ɗora sakamakon zaɓe a INEC”, in ji Jungudo.

Haka kuma, ADC ta ce ta kammala dukkan ayyukanta, amma ta jaddada cewa har yanzu tana cikin tsarin lokaci da ƙa’idojin INEC na miƙa sunayen ƴan takarar da aka zaɓa.

A yayin da yake magana da ƴan jarida, sakataren yaɗa labarai na ADC, Malam Bolaji Abdullahi, ya ce jam’iyya ta kammala dukkan ayyuka, ciki har da zaɓen ƴan takara na jam’iyyar da za su fafata a zaɓen 2027, amma tana jirar lokaci ne kawai.

Ita kuwa jam’iyyar LP ƙarƙashin jagorancin, Nenadi Usman ta ce ta amince da ƴan takarar 1,211 a hukumance domin yin takara a muƙamai daban-daban a zaɓen 2027.

Sakataren yaɗa labarai na ƙasa na jam’iyya, Ken Asogwa, ya ce kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ya amince da dukkan ƴan takarar da aka zaɓa a zaɓen fitar da gwani, kuma jam’iyyar za ta fara ɗora sunayensu a shafin a INEC a ranar 28 ga Yuni.

siyasa
Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

MASU ALAKA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
Tambarin Dimokuradiyya

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

September 5, 2026
Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
Tambarin Dimokuradiyya

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

September 4, 2026
Ko INEC Na Da Hannu A Rikice-rikicen Jam’iyyun Siyasa A Nijeriya?
Tambarin Dimokuradiyya

INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027

August 28, 2026
Next Post
Babban Ruhin Kafa Jam’Iyyar JKS: Me Ya Sa Jks Ta Iya Samun Gaggarumin Nasara

Babban Ruhin Kafa Jam'Iyyar JKS: Me Ya Sa Jks Ta Iya Samun Gaggarumin Nasara

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.