Shawarar da Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta ba ƴan Nijeriya na rungumar ƙananan sana’o’in gargajiya kamar su ƙosai, gasasshiyar masara da ƙuli-ƙuli, na ci gaba da jan hankalin jama’a a faɗin ƙasar nan.
Kalaman da ta yi a daidai lokacin da ake fuskantar tashin farashin kayan abinci, rashin aikin yi da matsin tattalin arziki, sun wuce zama batu na siyasa kawai. Sun kuma haifar da zurfafa tunani kan muhimmancin sana’o’in da ba na gwamnati ba da kuma hanyoyin rayuwa da miliyoyin ƴan Nijeriya ke dogaro da su.
Yayin da masu suka da masu goyon baya ke ci gaba da musayar ra’ayi kan ma’anar da tasirin kalaman nata, binciken da LEADERSHIP Weekend ta gudanar a jihohi bakwai ya nuna gaskiya guda ɗaya: sana’ar ƙosai da ƙuli-ƙuli ba ƙaramar sana’a ce kawai ba, illa babbar hanyar samun abin rayuwa ga dubban iyalai.
A bayan tukwanen suya, duwatsun niƙa da buhunan gyaɗa akwai wata babban tattalin arziki ta ɓangaren da ba na gwamnati ba, wadda ta daɗe tana ɗaukar nauyin karatun yara, gina gidaje, ciyar da iyalai da kuma samar da ayyukan yi tsawon shekara, musamman a al’ummomin da damar samun aikin yi na hukuma ke da ƙaranci.
Daga jihohin Biniwe, Katsina, Zamfara, Filato, Neja, Nasarawa zuwa Kano, masu sana’ar sun bayyana irin ƙalubalen da suke fuskanta, waɗanda suka haɗa da tsadar kayan aiki, matsalar tsaro, rashin ingantacciyar wutar lantarki da kuma ƙarancin samun rancen kuɗi mai sauƙi.
A dukkan wuraren da aka ziyarta, masu samar da ƙuli-ƙuli da ƙosai da masu sayar da su sun amince kan abu guda: idan gwamnati ta tallafa musu da rancen kuɗi mai sauƙi, ingantattun na’urorin sarrafa kayayyaki da kuma tabbatacciyar wutar lantarki, sana’ar ƙuli-ƙuli da ƙosai za ta iya zama babbar hanyar samar da ayyukan yi a ɓangaren tattalin arzikin da ba na gwamnati ba a Nijeriya.
“Da sanar ƙuli-ƙuli na ta ɗauki nauyin karatun ƴaƴana”
A kasuwar Katsina-Ala da ke Ƙaramar Hukumar Katsina-Ala a Jihar Biniwe, Amina Sani, ƴar asalin Jihar Jigawa, ta shafe shekara 10 tana sana’ar sayar da ƙuli-ƙuli.
Ta ce wannan sana’a ita ce ginshiƙin rayuwar iyalinta, domin ta hanyar kuɗin da take samu ne ta ɗauki nauyin karatun ƴaƴanta maza biyu har suka kammala jarabawar SSCE, kuma yanzu suna jiran samun gurbin shiga manyan makarantu.
Ta ce: “Sana’ar ƙuli-ƙuli ta masu haƙuri ce. Yawan tallace-tallace na yau da kullum yana dogara da wurin kasuwa da kuma yawan kwastomomi. A rana ta yau da kullum ina samun ribar tsakanin Naira 2,000 zuwa 3,000.”
Ta bayyana cewa ribar kasuwancin na bambanta daga rana zuwa rana, amma ci gaba da yin sana’ar ba tare da yankewa ba ne ke tabbatar da ɗorewarta.
“A wasu lokutan ina samun har Naira 5,000 a rana, amma ba kullum ba ne. Ina haɗa sayar da ƙuli-ƙuli da man gyaɗa da kuma kayan lambu. Kuɗin da nake samu daga waɗannan sana’o’i ne nake biyan kuɗin karatun ƴaƴana da kuma kuɗin haya.”
Ga Ibrahim Idris mai shekara 13 kuwa, wannan sana’a ita ma ta zama hanyar rayuwa da kuma tushen fata.
Ya ce: “Ina zaune tare da iyayena a Unguwar Hausawa. Ina taimaka musu wajen sayar da ƙuli-ƙuli da sauran kayayyaki. Daga wannan sana’ar muke samun abinci da kuma biyan kuɗin haya.”
Ya ƙara da cewa karatu na ci gaba da kasancewa cikin shirin iyalinsu.
“Wani lokaci muna sayen ƙuli-ƙuli daga masu samarwa, wani lokaci kuma mahaifiyata ce ke sarrafa shi.”
Wata ƴar kasuwa, Mary Onoja, ta bayyana sana’ar a matsayin mai ɗorewa amma mai tafiya a hankali.
Ta ce: “Ba za ka yi arzikin gaggawa daga sana’ar ƙuli-ƙuli ba. Sana’a ce da ke kawo riba sannu a hankali. Kuɗin da muke samu daga gare ta ne muke ciyar da iyali tare da biyan buƙatun yau da kullum. Kamar kowace sana’a, ita ma tana da nata ƙalubalen.”
“Na samar wa mutum 15 aikin yi ta hanyar sana’ar ƙuli-ƙuli”
A Jihar Katsina, Alhaji Bishir Rahamawa, gogaggen mai sana’ar ƙuli-ƙuli da ya shafe sama da shekara 40 yana wannan harkar, ya ce sana’ar ce ta gina rayuwarsa gaba ɗaya.
Ya bayyana cewa ya gaji sana’ar ne daga mahaifinsa, kuma tun daga lokacin bai taɓa barinta ba.
Ya ce: “Na ci abinci, na yi aure, na ɗauki nauyin karatun ƴaƴana, kuma na kula da iyalina ta hanyar wannan sana’a. Ban san wata sana’a ba face sarrafa ƙuli-ƙuli.”
A halin yanzu, cibiyar sarrafa ƙuli-ƙulin tasa tana ɗaukar ma’aikata sama da 15, waɗanda ke aikin soyawa, niƙawa, tace man gyaɗa da kuma tattara ƙuli-ƙulin cikin ledoji.
Sai dai ya ce tsadar makamashi na ci gaba da rage ribar kasuwancin.
“Ina kashe kusan Naira 40,000 a kullum wajen sayen iskar gas saboda rashin tabbatacciyar wutar lantarki,” in ji shi.
Ita ma wata ƴar kasuwa, Amina Ya’u, cewa ta yi, sana’ar ita ce tushen biyan buƙatun gidanta.
Ta ce: “Wannan sana’a ce ke samar mana da abinci, tufafi, tare da biyan buƙatun ƴaƴana.”
Muna ci gaba da rayuwa ne ta hanyar bashin kasuwanci da ƙaramar Riba
Jihar Zamfara, masu sana’ar ƙuli-ƙuli sun ce matsalar tsaro da hauhawar farashin kayayyaki sun ƙara wahala wajen gudanar da sana’ar.
Fatima Mohammed, wadda ke sayar da ƙuli-ƙuli a Gusau, ta ce farashin gyaɗa ya yi tashin gwauron zabi.
Ta ce: “Babban mudun gyaɗa yanzu yana kai kusan Naira 2,000. Noma ma ba ya da sauƙi saboda matsalar rashin tsaro.”
Ta ƙara da cewa a yanzu yawancin masu sana’ar suna gudanar da kasuwancinsu ne ta hanyar karɓar kaya bashi.
“Muna karɓar gyaɗa bashi, mu sarrafa shi ya zama ƙuli-ƙuli, mu sayar sannan mu biya masu ba mu kayan. Ribar da nake samu a wata tana tsakanin Naira 10,000 zuwa 13,000.”
Wata ƴar kasuwa, Hadiza Dosara, ta ce ta fara haɗa sana’ar sayar da gyaɗa domin ta ci gaba da rayuwa.
Ta ce: “Sana’ar ƙuli-ƙuli ba ta da riba kamar yadda mutane da yawa ke zato. Ina samun ribar tsakanin Naira 28,000 zuwa 35,000 a wata. Da ba don amfanin gonar mijina ba, da rayuwa ta yi mini tsauri.”
Ta kuma bayyana cewa akwai lokutan da tallace-tallace ke raguwa sosai.
“Yawanci kasuwanci kan yi rauni ƙwarai a watan Ramadan,” in ji ta.
“Yanzu maza da mata sun dogara da sana’ar ƙuli-ƙuli don su rayu”
A birnin Jos ta Jihar Filato, masu sana’ar ƙuli-ƙuli sun ce yanzu sana’ar ta zama hanyar samun abin masarufi ga maza da mata baki ɗaya.
Usman Bello, mai shekara 59, ya ce ya fara sana’ar ne bayan da gobara ta ƙone shagon kayan masarufinsa.
Ya ce: “Na zauna a gida ba na yin komai har sai da ƴar’uwata ta ba ni shawarar na fara sana’ar ƙuli-ƙuli. Yanzu ina iya biyan kuɗin karatun ƴaƴana.”
Ya bayyana cewa kuɗin fara sana’ar na tsakanin Naira 150,000 zuwa 250,000, gwargwadon yanayin kasuwa da lokacin shekara.
“Ina samun ribar tsakanin Naira 30,000 zuwa 40,000 a wata,” in ji shi.
Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta tallafa wa masu sana’ar ta hanyar ba su rancen kuɗi ba tare da ruwa ba.
Shi ma Adamu Shuaibu, mai shekara 29, ya ce yanzu maza sama da 20 suna gudanar da sana’ar ƙuli-ƙuli a kasuwarsu.
Ya ce: “Ina samun ribar tsakanin Naira 25,000 zuwa 30,000 a wata. Wannan sana’a ba ta mata kaɗai ba ce.”
Isah Ahmed, wanda ya yi magana a madadin matarsa, ya ce sana’ar sayar da ƙuli-ƙuli a jumulla ma tana da amfani sosai.
Ya ce: “Matata tana samun ribar tsakanin Naira 40,000 zuwa 50,000 a wata ta hanyar sayar wa ƴan kasuwa masu talla.”
Tattalin Arzikin rayuwa da aka gina kan sana’ar gyaɗa
A Jihar Neja, wadda aka fi sani da kasancewa ɗaya daga cikin cibiyoyin samar da ƙuli-ƙuli a Nijeriya, masu sana’ar sun ce har yanzu wannan sana’a ita ce ginshiƙin tattalin arzikin iyalai da dama.
Fati Jibrin Banma ta ce: “Idan muka sarrafa mudu 30 na gyaɗa, muna samun ribar tsakanin Naira 10,000 zuwa 15,000.”
Shi kuma Gambo Mohammed cewa ya yi yawan kuɗin da ake samu yana bambanta daga rana zuwa rana.
Ya ce: “Idan na yi dace a rana ina samun ribar tsakanin Naira 3,000 zuwa 4,000, amma a wasu lokutan ma ana iya yin asara.”
Ita ma Hadiza Musa ta ce duk da cewa ribar ba ta da yawa, sana’ar tana da ɗorewa kuma ana iya dogaro da ita.
Ta ce: “Ina samun kusan Naira 5,000 daga sarrafa mudu 10 na gyaɗa. Haka kuma ina kai ƙuli-ƙuli zuwa Abuja da Legas domin sayarwa. Sana’a ce mai ɗorewa.”
“Tana raya gidaje kuma tana hana matasa zaman banza”
A birnin Lafia na Jihar Nasarawa, masu sana’ar ƙuli-ƙuli sun ce wannan sana’a na taimakawa iyalai wajen samun abin rayuwa, sannan tana samar wa matasa aikin yi tare da hana su zaman kashe wando.
Malama Zainab Musa, wadda ta shafe shekara 30 tana sana’ar, ta ce: “Ta hanyar sana’ar ƙuli-ƙuli nake biyan kuɗin makaranta, kuɗin haya, tare da ciyar da iyalina.”
Ta bayyana cewa ta fara sana’ar ne da ƙaramin jari ta hanyar karɓar gyaɗa bashi.
Ta ce: “Na fara ne da karɓar gyaɗa bashi, ina soyawa ina sayarwa, sannan a hankali nake tara jari har sana’ar ta bunƙasa.”
Sana’ar ƙuli-ƙuli na tallafa wa iyali kuma tana ɗaukar nauyin ilimi
Ga masu sana’a da dama a Kasuwar Yan-Kura da ke Jihar Kano, ƙaramin abin ci na gargajiya wato ƙuli-ƙuli, wadda ake yi da gyaɗa, ya wuce zama abin ci kawai, ya zama ingantacciyar hanyar samun abin rayuwa, ɗaukar nauyin ilimi, tallafa wa iyalai da kuma samar da ayyukan yi.
Duk da ƙalubalen tattalin arziki, masu sana’ar sun ce sun gina kasuwanci mai ɗorewa a kan sayar da ƙuli-ƙuli. Wasu daga cikinsu na samun ribar dubban Nairori a kullum, lamarin da ke ba su damar ciyar da iyalansu da kuma ci gaba da gudanar da ƙananan sana’o’insu.
Khadijat Ibrahim, wadda ta shafe kusan shekara takwas tana wannan sana’a, ta ce tana kashe kusan Naira 20,000 a kullum wajen sayen ƙuli-ƙuli, kuma galibi tana sayar da duk kayan nata kafin ƙarshen kasuwa.
A cewarta, tana samun ribar kusan Naira 5,000 a kullum, inda take saka wani ɓangare na ribar a sana’ar sayar da alawa, yayin da sauran kuɗin take amfani da su wajen tallafa wa iyayenta.
Maryam Yusufa, mai shekara 18, wadda ta kwashe shekara bakwai tana sana’ar, ta ce ta koyi harkar ce daga mahaifiyarta, kuma yanzu tana sayar da ƙuli-ƙuli da gyaɗa.
Ta bayyana cewa tana kai kayan da darajarsu ta kai tsakanin Naira 10,000 zuwa 15,000 kasuwa a kullum, kuma tana iya samun ribar har Naira 3,000 daga duk kayan da suka kai Naira 10,000 da ta sayar.
Maryam ta ƙara da cewa sana’ar ta ba ta damar haɗa kasuwanci da karatun boko da na addini, tare da taimakawa wajen kula da iyalinsu.
Ta ce: “Wannan sana’a ta ba ni damar haɗa kasuwanci da karatun boko da na addini, tare da ba da gudummawa wajen kula da iyalina.”
Ta kuma yi kira ga matasan da ba su da aikin yi da su rungumi ƙananan sana’o’i maimakon zaman banza.
Ita kuwa Aisha Dan-Jummai, mai shekara 65, wadda ta shafe shekara 25 tana sana’ar ƙuli-ƙuli, ta ce wannan sana’a ta sauya rayuwar iyalinta gaba ɗaya.
Ta bayyana cewa kuɗin da take samu daga sana’ar ne ya ba ta damar ciyar da iyalinta, taimaka wa ƴan uwanta, ɗaukar nauyin karatun ƴarta mai shekara 16, da kuma aurar da ƴaƴanta uku.
Ta kuma bayyana cewa ta koyar da ɗanta mai shekara 25 wannan sana’a, wanda yanzu ya shafe kusan shekara bakwai yana gudanar da kasuwancinsa da kansa.
Ta ce: “A ranakun kasuwa masu albarka, ina sayar da kaya har Naira 40,000, kuma ina samun ribar kusan Naira 10,000.”
Ta ce hakan ya nuna irin muhimmancin tattalin arzikin da sana’ar ƙuli-ƙuli ke da shi ga al’ummar Jihar Kano.
Yadda muka gina gidaje kuma muka ɗauki nauyin ýanƴanmu har matakin digiri da sana’ar ƙosai
Da sanyin safiya, tun kafin ketowar alfijir yayin da mutane da dama ke barci, Misis Ashe Ojomo ta riga ta tashi tana ɓare wake da shirya kayan haɗin ƙosai domin fara sana’arta ta yau da kullum.
Misis Ojomo, wadda ta shafe shekara 22 tana sana’ar, ta yi nasarar ɗaukar nauyin karatun ƴaƴanta uku har suka zama masu digiri. Asalinta ƴar Jihar Kogi ce, kuma tana sayar da ƙosai a wata mashahuriyar tashar mota da ke yankin Iyana Ipaja a Jihar Legas.
Haka kuma, rayuwar Madam Chibuzor ma tana tafiya ne da irin wannan tsari, inda take gudanar da sana’arta kullum sai dai a ƙarshen mako. Yawancin kwastomominta ma’aikata ne da ke aiki a Legas Island, waɗanda kan fara yin layi tun daga ƙarfe 6:30 na safe domin sayen ƙosai da burodi ko doya soyayya a kusa da Nigerian Eɗchange da ke yankin CMS.
Bayan shafe sama da shekara 24 tana sana’ar, Chibuzor ta ce nasararta ba za a auna ta da tsawon lokacin da ta yi tana tsaye a gaban murhun soya ba.
Duk da cewa ta rasa mijinta kusan shekara huɗu da suka gabata, ta ci gaba da tafiyar da sana’ar cikin nasara.
Ta ce: “Ina gode wa Allah domin bai bar ni ni kaɗai ba. Na samu nasarori masu yawa har ban ma san ta inda zan fara lissafa su ba.”
Ta ba da labarin yadda ta fara sana’ar. “Na fara ne da gwagwarmaya. Budurwar ƙanin mijina ce take sayar da ƙosai a nan tsibirin Legas, yayin da ni kuma nake gudanar da sana’ata a Alapere. Daga baya ta bar wurin ta ba ni. Ita ce ke sayo kayan haɗi, ni kuma nake sayarwa, sannan muna raba riba; kaso biyu nawa ne, kaso ɗaya nata. Daga nan ne komai ya fara.”
Ta ce daga wannan ƙaramar farawa ta gina sana’a mai ɗorewa da ke kula da iyalinta.
“Na kai ƴaƴana biyu makaranta ta hanyar wannan sana’a. Babbar ƴata ta kammala karatu a Jami’ar National Open Uniɓersity da ke Abeokuta, yayin da ƙaramar ƴata ke karatu a Jami’ar Jihar Legas (LASU).”
Ta kuma bayyana cewa ita da marigayin mijinta sun gina gida a Ikorodu kafin rasuwarsa.
“Mun gina gidanmu a Ikorodu da ke Legas, inda nake zaune yanzu. Ko da ban mallaki mota ba, ina da gida na kaina, kuma ina gode wa Allah.”
A cewarta, gamsuwa da abin da Allah Ya ba mutum ita ce sirrin rayuwa.
“Ba na son kwaɗayin rayuwa. Ina rayuwa ne rana zuwa rana, kuma ina gode wa Allah da abin da Ya azurta ni.”
Sai dai ta jaddada cewa sana’ar ba mai sauƙi ba ce.
Ta ce tana tashi tun ƙarfe 3:00 na asuba, tana shirya kayan abinci har zuwa kusan ƙarfe 7:00 ko 8:00 na safe kafin fara sayarwa.
“Sana’ar ƙosai ba ta ragwaye ba ce. Dole mutum ya kasance mai jajircewa.”
Ta kuma yi magantu kan tashin farashin kayayyaki.
“Yanzu niƙa derika ɗaya na wake ta kai kusan Naira 700. Wake, barkono da mai duk sun yi tsada sosai. A da ina iya biyan kuɗin haya na shago, amma yanzu ribar ba ta isa ta biya haya ba.”
Ko da yake tana samun kuɗin tallace-tallace tsakanin Naira 60,000 zuwa 80,000 a rana, ta ce mutane da yawa suna rikita yawan kuɗin shiga da riba.
“Ina tattara duk kuɗin da na samu, sannan duk mako ina sake sayen kayan sana’a. Abin da ya rage ne kawai nake amfani da shi ni da ƴaƴana.”
Duk da ƙalubalen da ake fuskanta, ta ce sana’ar ta ba ta mutunci da manyan nasarori.
“Ni mai digiri ce, kuma ta hanyar wannan sana’a na ɗauki nauyin karatun mutum uku har suka zama masu digiri. Haka kuma na gina gidaje a Legas da kuma garinmu na asali.”
Ƙalubalen da Ke Addabar Sana’ar

Ifeanyi, mai sana’ar ƙosai a Sango Ota na Jihar Ogun, ya ce tashin farashin kayayyaki da kuma cin zarafin da jami’an gwamnati ke yi musu na ƙara jefa sana’ar cikin ƙalubale.
Ya ce: “Ƴansanda da jami’an KAI (hukumar kula da bin dokoki) kan zo su ƙwace mana kayanmu. Wani lokaci har muna rasa duk ribar da muka samu cikin mako guda.”
Ya ƙara da cewa duk da cewa bai gina gida ko sayen mota ba, sana’ar na ci gaba da ɗaukar nauyin rayuwarsa.
“Aƙalla ina samun abin da zan ci a kullum, ina kuma biyan kuɗin makarantar ƴaƴana da kuɗin haya.”
Haka ita ma Shakirat, uwa mai renon ƴaƴa ita kaɗai, ta ce ta fara sana’ar ne da kwanon tumatir ɗaya na wake da lita biyar na mai, kuma duk da hauhawar farashin kayayyaki ta ci gaba da dogaro da sana’ar.
Ta ce: “Wake da ake saye kan Naira 40,000 a da, yanzu ya haura Naira 90,000. Farashin gas da mai na ci gaba da tashi, amma muna gode wa Allah.”
Ta bayyana cewa cire tallafin mai ya ƙara tsananta tsadar gudanar da sana’ar, amma har yanzu ita ce kawai hanyar samun abin rayuwarta.
A faɗin Nijeriya, sana’o’in ƙosai da ƙuli-ƙuli na ci gaba da zama ginshiƙin tattalin arzikin da ba na gwamnati ba, inda suke zama hanyar rayuwa ga miliyoyin iyalai.
Ko da yake ribar sana’o’in ba ta da yawa kuma ba ta tabbata a kowane lokaci ba, masu sana’ar sun ce ta ba su damar gina gidaje, ɗaukar nauyin karatun ƴaƴansu, samar da ayyukan yi da kuma kula da iyalansu duk da matsin tattalin arziki.
Kamar yadda wani ɗan kasuwa ya taƙaita: “Wataƙila ba za ta sa mu zama attajirai cikin dare ɗaya ba, amma tana ba mu damar ci gaba da rayuwa.”
Wani matashi mai shekara 30, wanda ya buƙaci a kira shi Daɓid kawai, ɗan asalin Yola a Jihar Adamawa, ya ce neman ingantacciyar rayuwa ne ya sa ya shiga sana’ar sayar da ƙosai da burodi, wadda yanzu ita ce tushen samun abin rayuwarsa.
A cewarsa: “Tun da na zo Legas a shekarar 2019, a kowace shekara na kan koma gida domin ganin iyalina, ko da rayuwa ta yi wahala. Amma bana abin ya bambanta. Wannan ne karo na farko da na shafe shekara ɗaya cif a Legas ba tare da komawa Yola ba. Ba abu ne mai sauƙi ba, musamman kasancewata ɗan fari.”
A tashar mota ta Berger, ɗaya daga cikin manyan hanyoyin shiga birnin Legas, Daɓid ne ke jagorantar wasu matasa huɗu, duk ƴan asalin Jihar Adamawa, a wurin sayar da ƙosai.
Ya ce: “Ko da yake ni ne ke kula da ayyukan yau da kullum kuma nake jagorantar yaran, muna da wata mace ce mai wannan sana’ar. Ita ce ta kasance tana soya ƙosai tana sayarwa kai tsaye ga kwastomomi kafin ta miƙa mana yawancin alhakin. Yin aiki a nan ya koya mini ladabi, haƙuri da yadda ake mu’amala da mutane iri-iri a kowace rana.”
Daɓid ya ce ko da wasu na kallon sana’ar ƙosai a matsayin ƙaramar sana’a, ita ce ta ba shi damar ciyar da kansa a babban birni kamar Legas.
Ya ƙara da cewa: “Da yake ni ne ɗan fari a gidanmu, kuma ƙannena ba sa tare da ni, dole ne in kula da kaina tare da tunanin yadda zan taimaka musu da ke gida.”
Yayin da yake nuna godiyarsa ga sana’ar, ya ce: “Ina godiya saboda wannan sana’a ta ba ni fata game da makomata. Da kuɗin da na samu na tara, ina shirin ɗaukar mataki na gaba a rayuwata. Da yardar Allah, zuwa ƙarshen wannan shekara ina shirin yin aure, kuma na yi imanin wannan sana’a ce ke taimaka mini wajen shimfiɗa tubalin wannan buri.”














