ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kano Ta Yi Zarra Wajen Kashe Kuɗi Don Raya Ilimi A Yammacin Afirka

by Idris Aliyu Daudawa
2 months ago
Kano

Jihar Kano ta kasance  jagora da aka ɗauke ta wadda ta ke yin abubuwa ko ayyukan da suka shafi  gwamnati a ƙungiyar ƙawancen tattalin arziki kan kashe kuɗin domin lamarin da ya shafi ilimi kamar dai yadda rahoton da Jami’ar Paris ta wallafa na shekarar 2026.

Rahoton ya bayyana Kano ta ɗaya daga cikin gwamnatoci 209 waɗanda suke daga ƙasashe 15 da suke ƴan ƙungiyar ne, inda aka bada misali da Jihar kan yadda take ci gaba da zuba jari sai kuma aiwatar da ayyuka kamar yadda suke a cikin kasafin kuɗi na ilimi.

Yadda Jihar Kanon ta kasance ta ɗaya ya biyo bayan ganin yadda ta bayyana aniyarta ta kafa dokar ta ɓaci kan lamarin da ya shafi ilimi,tsarin da ƙarin kuɗi  ɓangaren ilimi  ya biyo bayan shi, samar da ayyukan da za su kyautata jin daɗin karatu,ɗaukar Malaman makaranta da horad da su, sai kuma ƙoƙarin da gwamnatin ta ke na samar da hanyar samun ilimi mai inganci.

ADVERTISEMENT

Kamar yadda rahoton ya nuna,Kano ta samu gaggarumin ci gaba wajen samun babban maki na ayyukan da ake kashe kuɗi don bunƙasa ilimi inda ake amfani da ma’aunin Indeɗ (S-WAESI) abinda ya bata damar samun maki 87.21, inda ta yi ma wasu da yawa waɗanda ake yi masu kallon kamar sun fi kowa dangane da hakan ya satafi sauran wasu gwamnatocin ƙasashe da suka haɗa da, Dakar da kuma Saint-Louis a Senegal. JIhar Legas ce ta ke bi mata, inda ta zama ta 16 a lamarin yadda ake hisabin na sashen yammacin Afirka.

Shi tsarin na S-WAESI yana kallon yadda gwamnatoci sukje mai da hankali kan lamarin ilimi ta hanyar amfani da wasu abubuwan da suka haɗa da yadda aka kashe kuɗin na ɓangaren ilimi,nawa ne ake kashe ma kowane ɗalibi, yadda ake aiwatar da kasafin kuɗin,kashi nawa aka ware ma ilimi, yin abin da gaskiya da kuma sheda kamar yadda aka bada rahoto.

LABARAI MASU NASABA

An Tantance Masu Neman Aikin Koyarwa 500 A Jigawa

JAMB Ta Ƙara Wa’adin Amincewar Guraben Karatu Zuwa 30 Satumba

Ƙarƙashin yadda aka aiwatar, da kashe kuɗin kan lamarin da ya shafi ilimi shi ne ya ke ɗauke da babban maki mai nauyin 35, sai mai bi ma shi, ko nawa  ake kashe ma kowane ɗalibi yana da 25, yadda ake aiwatar da kasafin kuɗin na da 20 yayin da kuma yadda ake ba lamarin ilimi muhimmanci, da sa gaskiya da riƙon amana na asusun kuɗin ko wannensu na da goma-goma.

Rahoton na Jami’ar ta Paris ya bayyana yadda Jihar Kano ta yi har ta kasa da yin  zarra wajen zama jagora wajen mizani kashe kuɗi ƙwarai da gaske babu kama hannun yaro wajen gani da sanin muhimmancin  ilimi shi ne wani ginshiƙin rayuwa, har ta ke kashe maƙudan kuɗaɗe ta hanyar aiwatar da kasafin kuɗin da aka amince a kashe saboda harkar ilimi, shi ya sa ma tafi kowace Jiha ta kashe kuɗi domin raya ilimi, gaba ɗaya a cikin Jihohin ƙasashen ƙawance  na yammacin Afirka  wato ECOWAS a taƙaice.

Shi nazarin ya shafi Jihohi, larduna, ƙaramin lardi, sai kuma wuraren da suke da matakain tamkar ƙaramar hukuma na ƙasashen Nijeriya, Senegal, Ghana, Côte d’Iɓoire, Saliyo, Laberiya, Benin, Burkina Faso, Mali, Nijar, Togo, Guinea, Guinea-Bissau da kuma Cabe Ɓerde.

Kashe kuɗaɗe  masu yawa a tsarin Jihar Kano ya ƙaru ne sannu a hankali a cikin ƴan shekaru ba wasu yawa ba ne. Gwamnatin Jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ware ma ɓangaren  na ilimi kashi 29.5 na kasafin kuɗin Jihar na shekara ta 2024, ta haka ne har ya amince abin ya kai kashi 30  na kasafin kuɗin shekarar 2025, inda ya nuna cewa lalle cewar gwamnatin ta nuna ɓangaren ilimi yana daga cikin abubuwan da ta fi ba muhimmanci idan lamarin kashe kuɗaɗen ta ya taso domin raya al’umma.

Kano
Idris Aliyu Daudawa
+ postsBio
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tarihin Rayuwar Galadiman Kano Alhaji Tijjani Hashim (2)
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kyamar Baƙi: An Sake Kwaso Ƴan Nijeriya 83 Daga Afirka Ta Kudu
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kamfanin Simintin Dangote Ya Tallafa Wa Manoma 60 Da Kayan Aiki A Edo
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tsohon Shugaban Ƙasa Jonathan Ya Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Ƙasa 18 A Jihar Bauchi

MASU ALAKA

Kano
Ilimi

An Tantance Masu Neman Aikin Koyarwa 500 A Jigawa

August 31, 2026
Kano
Ilimi

JAMB Ta Ƙara Wa’adin Amincewar Guraben Karatu Zuwa 30 Satumba

August 29, 2026
ASUU Na Barazanar Shiga Yajin Aiki A Jami’o’in Jihohi 11 Kan Rashin Biyan Alawus-alawus
Ilimi

ASUU Na Barazanar Shiga Yajin Aiki A Jami’o’in Jihohi 11 Kan Rashin Biyan Alawus-alawus

July 3, 2026
Next Post
NAF Ta Kai Hare-Haren Sama Kan Maboyar Ƴan Ta’adda A Borno

NAF Ta Kai Hare-Haren Sama Kan Maboyar Ƴan Ta'adda A Borno

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.