ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Dauda Ya Raba Buhunan Taki 72,000 Da Kayan Noma Kyauta Ga Manoman Zamfara

by Sulaiman
2 months ago
Taki

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da rabon buhunan taki 72,000 kyauta tare da magungunan kashe ciyawa da sauran kayan aikin noma ga manoma a faɗin jihar, a wani mataki da gwamnatin jihar ta ce na ƙara bunƙasa harkar noma da tabbatar da wadatar abinci.

An ƙaddamar da shirin rabon takin daminar shekarar 2026 ne a ranar Juma’a a Trade Fair Complex da ke Gusau, babban birnin jihar.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta raba buhunan taki 72,000, lita 200,000 na magungunan kashe ciyawa, da kuma injuna 100 na sarrafa ragowar amfanin gona.

ADVERTISEMENT
Taki

Sanarwar ta ƙara da cewa, an kuma samar da injuna 100 na yankan ciyawar kiwo, injuna 100 na niƙa abincin dabbobi, iri na ingantacciyar ciyawar kiwo, babura 20 da wayoyin hannu 20 domin jami’an ba da shawara kan harkokin noma.

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Lawal ya ce Zamfara na daga cikin jihohin da ke da muhimmiyar rawa a fannin noma a Niueriya saboda yalwar ƙasar noma da kuma ƙwazon al’ummarta.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Ya ce, rabon kayan aikin noman wani sabon mataki ne na cika alƙawarin gwamnatinsa na farfaɗo da harkar noma, ƙarfafa wadatar abinci, samar da hanyoyin dogaro da kai ga al’umma da kuma mayar da Zamfara ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin noma a ƙasar.

A cewarsa, noma shi ne ginshiƙin tattalin arzikin jihar, kuma yana taka muhimmiyar rawa wajen rage talauci, yaƙi da ayyukan ‘yan bindiga da sauran laifuffuka.”Noma ba kawai hanyar samun kuɗi ba ce, yana cikin tarihinmu da al’adunmu, kuma shi ne tubalin da za a gina cigaban da al’ummarmu za su ci gaba da amfana da shi a nan gaba,” inji gwamnan.

Taki

Lawal ya bayyana cewa burin gwamnatinsa shi ne sauya noma daga tsarin dogaro da kai zuwa noma na zamani da ke amfani da fasaha tare da mayar da hankali kan kasuwanci.

Ya ce hakan za a cimma ne ta hanyar samar da ingantaccen taki da iri, amfani da injinan noma, bunƙasa ban ruwa, ƙarfafa ayyukan jami’an wayar da kan manoma, amfani da dabarun noma masu dacewa da sauyin yanayi da kuma samar da kasuwannin sayar da amfanin gona.

Gwamnan ya ce da dawowar zaman lafiya a wasu yankunan jihar, ƙarin al’ummomi na komawa gonakinsu, yayin da iyalai ke sake farfaɗo da hanyoyin samun abin dogaro.Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta nuna jajircewarta ba ta baki kaɗai ba, har ma ta hanyar haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya, abokan hulɗar ci gaba da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, tare da biyan kuɗaɗen da suka rataya a wuyanta domin tabbatar da jihar ta ci gajiyar shirye-shiryen bunƙasa noma.

A cewarsa, shirye-shirye irin su FADAMA III, NG-CARES, SPIN, ZACADEP, SAPZ, da shirye-shiryen da Asusun IFAD ke tallafawa sun taimaka wa dubban manoma da ingantattun iri, taki, magungunan noma, kayan ban ruwa, kayan aikin gona da kuma ilimin noma na zamani.

Ya ce waɗannan tsare-tsare na ƙara yawan amfanin gona, faɗaɗa gonaki da bunƙasa kuɗaɗen shiga na gidaje, tare da gina tubalin samar da ingantaccen tsarin noma mai jure sauyin yanayi.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa rabon takin da sauran kayan aikin noman zai shafi dukkan mazabu 147 na siyasa da ke ƙananan hukumomi 14 na jihar.

A ƙarƙashin tsarin rabon, kowace mazaba za ta karɓi buhunan taki 340, yayin da kowace ƙaramar hukuma za ta samu lita 8,000 na magungunan kashe ciyawa.

Taki
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Kano Ta Yi Zarra Wajen Kashe Kuɗi Don Raya Ilimi A Yammacin Afirka

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.