Babban Alƙalin-alƙalai a Jihar Kaduna, Mai Shari’a Muhammad Tukur Mu’azu Aliyu, ya buƙaci alƙalai na kotunan Majistari na jihar, da su ci gaba da tura shari’o’i da suka dace zuwa cibiyar sulhu jihar (KDMDC).
Aikin cibiyar dai shi ne, sasanta masu taƙaddma, a ƙarƙashin shirin sulhu na ‘Alternatiɓe Dispute Resolution’ (ADR).
Muhammad ya yi kiran ne yayin ƙaddamar da taron mako na kotun jihar a hukumance na shekarar 2026.
Ya ce a ƙarƙashin shirin ADR, ana yin sulhu ba tare da ɓata wani tsawon lokaci ba da warware taƙamma a cikin kwanciyar hankali da lumana.
Ya yi kira ga duk masu wata taƙadda da su rungumi Shirin, maimakon ɓata dogon lokaci suna kai komo a kotu, inda ya yi nuni da cewa rungumar shirin ba wai wata gazawa ce a tsakanin masu taƙadda ba, amma shiri ne da zai samar masu da mafita ciki sauƙi.
Ya daganta tattaunawa a tsakanin masu taƙadda tamkar ginshiƙi ne na samar da zaman lafiya mai ɗorewa.
Babban Alƙalin-alƙalai na Jihar Kaduna yaba wa cibiyar KDMDC, musamman bisa nasarar ta da samu a sama da shekaru guda na warware ɗaruruwan taƙadda a jihar ta hanyar shiga tsakani da kuma yin amfani da shirin na ADR. Ya ce wannan nasarar ta ƙara ƙarfafa guiwar al’ummar jihar na ƙara ci gaba da amincewa da tsarin shari’a na jihar.
Shi kuwa a jawabin da ya gabatar, Kwamishin Shari’a kuma Atoni Janar na jihar, Sir James Kanyip, ya yi nuni da cewa rungumar tsarin ADR zai ƙara rage ɓata lokaci a kotuna da kashe kuɗaɗe a tsakanin masu taƙaddama da kuma ƙara ƙarfafa dangantaka a tsakanin masu taƙaddama.














