A zango na daya da rabi na shekarar 2026, Jiragen Ruwa da suka isa a tashoshin Jiragen Ruwan da ke kasar, sun kai adadin 2,300.
Wannan karin adadin na 2026, ya kai sama da kaso 6.9 2,152 na Jiragen Ruwa da suka isa a tashoshin Jiragen Ruwan da ke kasar a 2025.
Shugaban hukumar NPA Abubakar dantsoho, ya sanar da haka taron ganawa na karshen shekara na majalisar ta NPA da ya gudana a jihar Legas.
Taken taron shi ne, “Samar da hanyar saukin yin hada-hadar kasuwanci a tsakanin iyakokin kasa,“.
Masu ruwa da tsaki da dama a fannin, sun halarci taron, inda aka tattaua kan yadda za a kara daukar matakan kara karffaa fannin na sufurin Jiragen Ruwan kasar.
Babbar manajar kula da da kididdiga a NPA, Madam Okenwa Igwebuike ce, ta wakilci dantsho a wajen taron.
dantsho ya bayyana cewa, a karkashin tsarin yin rijistar zirga-zirgar manyan Jiragen Ruwa na GRT, manyan Jiragen da suka sauka a Tashoshion, sun karu daga kaso miliyan 20.9 zuwa kaso miliyan 96.6, idan aka kwatanta da na miliyan 79.9, da aka samu, a farkon rabin shekarar 2025.
Ya danganta wannan karuwar da aka samu bisa kara samun gudanar da ayyuka a Tashoshin at Lekki da na Onne.
Ya kara da cewa, manyan kayan da aka sauke a Tashohin, sun karu daga metric tan miliyan 60.8 a zangon farko na shekarar 2025 zuwa tan miliyan 68.2, wanda ya kai kaso 12.2.
Ya ci gaba da cewa, mayan kayan da aka shigo da su daga ketare zuwa cikin Tashoshin, sun karu daga tan miliyan 38.4, zuwa tan miliyan 36.3.
Kazalika, shugaban ya sanar da cewa, manyan kayan da dka fitar da su daga Tashohin, sun karu daga tan miliyan 23.5 zuwa tan miliyan 29.2.
Shugaban na NPA ya bayyana cewa, yawan kayan daka suka sauka a Tashar Lekki, sun kai kaso 40.
A cewarsa, an samu hakan ne, saboda karin gudanar da ayyukan matatar Mai ta dangote, gannin yadda ta samar da sama da kaso 76, musaman saboda rage cunkoson Jiragen Ruwan da ke sauka a Tashar.
Ya kara da cewa, an samu karin fitar da Iskar Gas samfarin LNG da Matatar ta dangote ta yi daga Tashar Onne, wanda ya kai 22.7, wanda wannan ya hada da wanda aka fitar, daga Tashoshin Kalaba da Riba, da ya kai kaso hudu.
dantsoho ya kuma sanar da cewa, shigar da Kwantaina ya karu daga kaso 10.3 zuwa kaso 815,236 wanda hakan ya nuna cewa, sun haura na daga 739,142 da aka yi a rabin shekarar 2025.
Ya ce, kayan da aka shigo da su ta hanyar TEU, sun kai 546,755 wanda hakan ke nuna cewa, an samu kason da ya kai 67, na yawan jimlar Kwantainar da aka shigo da su
dantsho ya kara da cewa, Kwantaina da aka fitar ta hanyar TEU kuwa, sun kai 203,980 wanda hakan ya nuna cewa, sun kai kaso 25.
A cewarsa, ta hanyar ta TEU hada-hadar shiga da fitar da kaya, sun karu daga kaso 169.5 zuwa kaso 35,574, wanda hakan ya kai kaso hudu, na yawan jimlar Kwantaina da aka aka yi.
Ya sanar da cewa, manayan ababen hawa da aka yi jigilarsu, sun yi matukar karuwa, daga kaso 42.5103,375 zuwa kaso 72,568 a 2025.
Shugaban ya danganta wannan karin, musamman saboda yawan ayyukan hada-hadar shige da ficen a Tashoshin kasar da kuma wanda kamfanin PTML ya gudanar a Tashar Tin Can.
dantsoho ya kara da cewa, hatta lokacin zuwan manyan Jiragen cikin Tashoshin bayyana cewa, ya karu zuwa kwanuka shida daga kwanukan biyar inda ya kara da cewa, wasu manyan Jiragen suma isar su zuwa cikin Tashoshin daga kaso 3.1 zuwa kaso 36.1.
A cewarsa, matatar Man dangote, ta taimaka wajen kara samar da sauyi na yawan ayyukan da ake gudanarwa a Tashoshin
Kazalika, ya bayyana cewa, shirin da matatar ta dangote ke yi na kara fadada, samar da Gangar Mai miliyan 1.4 a kullum zai bukaci karin a samar da kayan aiki a Tashoshin kasar da kuma tare da samar da daidaito na kara samar da haraji ga kasar nan.
Bugu da kari, dantsoho ya danganta karuwar shigo da Kwantaina zuwa cikin Tashoshin, kan karuwar ayyukan masana’antu da kuma samar da daidaito a bangaren bunkasa tattalin arzikin kasar nan, musamman, duba da irin kokarin da aka yi, a Tashar Onne.
A cewar shugaban, samar da hanyar saukin gudanar da hada-hadar zirga-zirgar Jiragen Ruwa a tsakanin kasashen da ke makwabtaka da Nijeriya, abu ne, da yake da matukar mahimmanci, da ya kamata kasar ta cimma.
Sai dai, shugaban hukumar ta NPA dantsoho ya danganta matsalar samun wadattun kudade da hukumar ke fuskanta, a matsayin abinda ke ci mata Tuwo a kwarya, musamman wajen gudanar da ayyukan gaggawa.
Ya bayyana cewa, kaso 50 da gwamnatin tarayya ke cirewa na kai tsaye daga hukuminta da ke gudanar da hada-hadar kasuwanci, ba za su wadaci hukumar ta NPA, wajen gudanar da ayyukan ta ba.
A saboda haka, shugaban ya bukaci taimakon masu ruwa da tsaki a fannin samar kudaden shiga da za su kai musamman ta hanyar kaso 80:20,inda hakan, zai kara taimaka wa hukumar, wajen ci gaba gudanar da ayyukan ta.
Kazalika, shugaban ya kuma jaddada mahimmancin ci gaba da yin hadaka da masu ruwan da tsaki a fannin musamman, na goyon bayan su, kan aikin da hukumar ke yi, na zamanantar da kayan aikin na NPA.
Suma a na su jawaban da ban da ban a wajen taron, wasu daga cikin masu ruwa da tsakin, sun bayyana gamsuwar su, bisa samar da kayan aiki na zamani da hukumar ta NPA ta yi.
A cewarsu, hakan ya kara taimaka wa kawar da kayan da aka shigo da su daga ketare zuwa cikin Tashoshin Jiragen Ruwan kasar da kuma samar da matakan da suka taimaka a bangaren samar da saukin gudanar da hada-hadar kasuwanci.
daya daga cikin masu ruwan da tsaki, shugaban hukumar kula da zirga-zirgar Jiragen kasa ta kasa NRC, Dakta Kayode Opeifa, ya bayyana cewa, an kusa kammala ayyukan da ake kan yi a Ijora, Moniya da kuma na Papalanto.
A cewarsa, ayyukan za su taimaka matuka wajen kara kawar da kayan da ake shigowa da su zuwa cikin Tashoshin Jiragen Ruwan kasar gaba. Opeifa ya kara da cewa, hukumar ta NRC ta kasa na kan gudanar da aikin fadada Layukan Dogo da a hada su da Tashoshin Jiragen Ruwa na Apapa da Tin Can Island ds kuma ta Lekki.
Ya ci gaba da cewa, karin samun tafiyar gudanar da ayyuan zirga-zirgar Jiragen kasa zai taimaka matuka wajen kara rage cunkoso daga Tashar Apapa- zuwa Oshodi.
A cewarsa, wannan ci gaban zai kara taimaka wa wajen gudanar da shigowa da kuma fitar da manyan kaya, a Tashoshin Jiragen Ruwan kasar.













