Marigayi Alh Mohammed Sani Gwarzo da aka fi sani da Alhaji Tumbuleke, ya rasu ne a ranar 11 ga watan Augustan 2026 a jihar Kaduna, bayan tsawon jinyya, inda ya rasu, yana da shekaru 86 a duniya.
Tumbuleke, fitacce ne, da ya yi shura a fagen wasan kwakwayo da yake fitowa, a shirin Gidan Kashe Ahu, da ake yadawa a wannan can shekaru a kafar Radiyon tarayya wato FRCN da kuma NTA da ke a Kaduna, tun a 1980.
A makon da ya gabata ne, Ministar Al’adu, yawon bude ido da kirkire-kiren bunkasa tattalin arzikin kasa, Hannatu Musa Musawa, ta je gidan marigayi da ke kan titin Adawa a Kaduna domin yiwa iyalansa ta’aziyya.
Bayan kammala ta’ziyyar a gidan mamancin ministar ta tattauna da ‘yan jarida, kan batun mutuwar ta Tumbuleke, sanayyar da ke tsakanin ta da shi, tunin ci gaba da kula da tarihi da gudunmawar da ya bayar a masana’antar a lokacin yana raye, musamman, a kasar Hausa da sauransu.
Wakilinmu ABUBAKAR ABBA, na cikin tawagar ‘yan jaidar a wajen hirar da ministar ta yi, ga yadda hirar ta kasance.
Wanne karin haske za ki yi kan wannan ziyarar da kika kowo a gidan marigayi Tumbuleke?
Toh …da farko dai, Allah ya jikan marigari Alh Mohammed Sani, Allah ubangiji, ya sa, ya huta, Allah ya sa, kaffara ce, domin na san ya dade, yana fama da ciwo.
Bayan haka kuma, aikinsa da ya yi, na hanyar wasan kwaikwayo ba da wannan na aikin da ya yi na hanyar yar da al’amari ko kuma bayar da gudunmawarsa wajen kirkire-kirkire a fannin wasan kwakwayo, abu ne wanda ke son mu gwamnatin tarayya, mu hada karfi da karfe, domin a kara fito da ayyukan da margayin ya yi, a fannin wasan kwaikwayo lokacin yana raye.
Ma’ana, wato mu kara farfado da shi, abinda za mu yi ke nan. Ni zan yi magana da mutanen da suka zauna da shi, lokacin yana raye, dama ya kamata in zauna da shi kuma mun dade, muna maganar zan zauna da shi, amma kamar yadda na ce, kana naka ne, Allah kuma na yin na sa, sai Allah bai nufa ba.
Duba da irin gudunmawar da ya bayar lokacin yana raye a wannan bangaren, a matsayin ki ministar ta ala’adu, akwai wani shiri da gwamnatin tarayya za ta yi, na karrama shi da iyalansa, domin a nuna irin gudunmar da ya bayar, musamman a wannan bangaren?
Kwarai da gaske, abinda zan iya gaya maka akwai, amma shirin, b azan iya fada kai tsaye, a nan ba, sai mun zauna da wadanda suka gaji irin tunanin na shi, na cewar mai ya kamata ayi, wanda idan an zauna, yanzu bazan sani ba, tunda ba a riga an zauna ba tukun.
Amma abinda zan tabbatar maka ko kuma in tabbatarwa da ‘yan Nijeriya shi ne, in Allah ya yarda gwamnatin tarayya, za mu zauna mu hada kai da wadanda suke kusa da shi, domin mu fito da irin tarihin da ya bari a baya, a fanin na wasan kwaikwayon, saboda idan ba mu yi hakan ba, zan iya cewa, mun zama butulu, saboda irin gudunmawar da ya bayar a fannin.
Marigayi Tumbuleke, ya bayar da gudunmawa, kuma tsakanin shi da Allah, domin ya sanya mutane a cikin farin ciki kuma zuciyarsa a bude take idan yana kan gudanar da wasan kwaikwayo, ba kuma wai, domin abinda za a bashi, ya ke yin saboda wasan kwakwayon ba, ya na yi ne, saboda kaunar Nijeriya, gwamnatin tarayya, dole ne a kan mu hakika, mu zo ba wai sababbin masu kirkire-kirkire ba, amma wadanda, suka assasa, kirkire-kirkiren, kila a samu kamar shi, wato mu hada kai muga yadda za mu taimaka.
Kamar da me za ki iya bayyana marigayi Tumbuleke musamman a fannin?
Tsakani da Allah, ba zan iya hada shi da wani a fanin wasan kwakwayo ba, musamman saboda irin basirar da Allah ya bas hi, ta nishadantar da masu kallo ba
A kwai mutane da yawa, da suka bayar da gudunmwarsu a fannin wasan kwakwayo, a Arewancin kasar, amma yanayin irin gudunmawar da shi Tumbuleke ya bayar lokacin yana raye, babu wanda ke a fannin, da bayar da irinta, tsakani da Allah ke nan, domin tun ina karama, Tumbuleke, koda raina ya baci, yana zanya ni dariya, ta hanyar kallon wasan kwakwayon sa, da yake gabatarwa.
Tumbuleke ya kawo wa, ‘yan Nijeriya, farin ciki, ta hanyar kallon wasan kwakwayonsa, Tumbuleke ya kawo haske a Nijeriya ya kawo haske a wannan masana’antar ta wasan kwaikwayo.
Ba zan iya, hada shi, da kowa a fannin wasan kwaikwayo ba, domin Tunbuleke da ban yake, domin haka dole, za mu hada kai domin muga yadda za ci gaba da tuna shi, kan irin gudunmwar da ya bayar, a masana’antar.
Wato ko ba a matsayinki na minista ba, mutuwar Tunbuleke ta taba ki ke nan?
Tabbas, mutwarsa ta taba ni, domin dan ma, bana kasar ya rasu, amma tsakani da Allah da samu labarin rasuwarsa, shi ya sa ma, kaga na shigo mota na taho, domin inzo, in yiwa iyalansa da ‘yan uwansa ta’aziyyar rashisa, domin idan ban zo yin ta’aziyyar rasuwar Tumbuleke ba, ai gwanda main dauki Tsintsiya ko Tabarma ta, in ninke, in koma gefe, ba ministar kere-kere ba, idan dai, Tumbuleke zai rasu, ace ban zo ba, Allah ya jikansa da rahama, amin.













