Ƙungiyar Dattawan Kiristoci ta Ƙasa (NCEF) ta buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kada ya sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a shekarar 2027, tana mai danganta hakan da abin da ta bayyana a matsayin “raunin gwamnatinsa wajen magance matsalolin tsaro da tattalin arziki.”
A gefe guda kuma, Arewa Think Tank ta soki NCEF kan kiranta ga Shugaba Tinubu da ya janye daga shirin sake tsayawa takara, tana mai cewa babu wata ƙungiyar addini da ke da ikon yanke wa ƴan Nijeriya hukuncin wanda za su zaɓa.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ƙarshen mako, wadda shugabanta, Dr. Samuel Danjuma Gani, ya sanya wa hannu, NCEF ta ce ana jagorantar ƙasar ne ta hanyar da ke haifar da ƙarin fargaba maimakon fata.
A cewar ƙungiyar, maimakon Shugaba Tinubu ya nemi wa’adi na biyu, ya kamata ya mayar da sauran lokacin mulkinsa wajen sake fasalin Nijeriya da kuma samar da sabon Kundin Tsarin Mulki.
Dattawan sun ce gwamnatin mai ci ta gaza cika nauyin da Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya ɗora mata na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ƴan ƙasa.
Sun kuma soki tsarin Musulmi da Musulmi da aka yi a takarar shugaban ƙasa, suna mai bayyana shi a matsayin abin da bai dace ba, musamman a lokacin da ƴan ta’adda ke ci gaba da kai hare-hare a wasu sassan ƙasar, inda Kiristoci da dama suka kasance cikin waɗanda rikicin ya shafa.
Sanarwar ta ce: “Hanyar da gwamnatin Tinubu ke bi wajen jagorantar ƙasa tana ƙara haifar da fargaba maimakon fata. Wannan yanayi ya sa masu kishin ƙasa ba su da wani zaɓi face su roƙi Shugaba Tinubu da kada ya sake neman wa’adi na biyu. Maimakon haka, ya kamata ya yi amfani da sauran lokacin mulkinsa wajen sake fasalin Nijeriya da kuma samar mata da sabon Kundin Tsarin Mulki, domin ya bar kyakkyawan tarihi.”
Dattawan Kiristocin sun kuma yi kira ga ƙabilu daban-daban, ƙungiyoyin al’adu da sauran ƙungiyoyin masu ruwa da tsaki da su fara shirye-shiryen tabbatar da amincewa da sabon Kundin Tsarin Mulki kafin babban zaɓen shekarar 2027.
Sun yi gargaɗin cewa kada a ɗauki haƙurin ƴan Nijeriya da wasa, suna mai cewa al’umma na matuƙar ɗokin ganin canji.














