ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, September 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Daƙile Yunƙurin Sace Ɗalibai Masu Zana Jarabawar WASSCE A Kogi

by Sulaiman
3 months ago
Kogi

Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai mummunan hari ranar Laraba a al’ummar Iluke-Bunu da ke karamar hukumar Kabba-Bunu ta jihar Kogi, inda suka kashe mutane uku a wani yunkuri na sace daliban da ke rubuta jarabawar kammala sakandare ta WASSCE.

A cewar mazauna yankin, maharan dauke da manyan makamai, wadanda aka ce sun zo akan babura kusan 40 kuma sanye da kayan sojoji, sun afka wa al’ummar da misalin karfe 10:00 na safe, suna harbe-harbe ba kakkautawa kafin su nufi makarantar Sakandare ta Gwamnati, Iluke, inda ake zana jarabawar.

Shaidun gani da ido sun ce maharan sun tarwatsa taron jarabawar tare da kokarin tursasa wasu daliban zuwa cikin daji. Sai dai saurin daukar mataki da jami’an tsaro suka yi ya hana afkuwar wannan babbar masifar.

ADVERTISEMENT

A cikin wata sanarwa da jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ’yansandan jihar Kogi, ASP Saliu Oyiza Afusat, ta fitar, rundunar ta ce ta samu kiran gaggawa cewa wasu ’yan bindiga masu yawa sun mamaye makarantar da nufin yin garkuwa da dalibai da mazauna yankin.

Sanarwar ta ce babban jami’in kula da rundunar ’yansanda ta Kabba “A” ya gaggauta tattara jami’ansa tare da dakarun rundunar PMF da tawagogin musamman na rundunar da ke jihar, gami da sojoji da jami’an sa-kai da ke aiki a yankin.

LABARAI MASU NASABA

Jami’an Tsaro Sun Ƙaddamar Da Aikin Ceto Limaman Da Aka Sace Bayan Taron APC A Zamfara 

Gwamna Fintiri, Dangote Da Sarakunan Gargajiya Sun Halarci Jana’izar Bamanga Tukur A Yola

Haɗaɗɗiyar tawagar tsaron ta fafata da maharan a wani kazamin musayar wuta, lamarin da ya tilasta musu tserewa zuwa cikin dazukan da ke kusa da yankin.

Kogi
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Jawabin Xi A Taron BRICS, Mafita Ce Ga Matsalolin Duniya
  • Sulaiman
    Duk Wani Yunkuri Na Karfafa Burin Japan Na Fadada Karfin Soji Zai Jefa Yankin Cikin Hadari
  • Sulaiman
    Tsohon Firaminsitan Jordan: Kasar Sin Tana Kan Gaba Wajen Gudanar Da Fasahar AI A Duniya
  • Sulaiman
    Hadin Gwiwar BRICS Na Jagorantar Hadin Kan Kasashe Masu Tasowa Da Dogaro Da Karfin Kansu

MASU ALAKA

Dansanda Ya Ki Karbar Cin Hancin Miliyan 1 Kan Ya Saki Wani Barawon Mutane A Kano
Manyan Labarai

Jami’an Tsaro Sun Ƙaddamar Da Aikin Ceto Limaman Da Aka Sace Bayan Taron APC A Zamfara 

September 14, 2026
Gwamna Fintiri, Dangote Da Sarakunan Gargajiya Sun Halarci Jana’izar Bamanga Tukur A Yola
Manyan Labarai

Gwamna Fintiri, Dangote Da Sarakunan Gargajiya Sun Halarci Jana’izar Bamanga Tukur A Yola

September 13, 2026
Tsohon Kwamishina A Gombe, Ya Marawa Pantami Baya
Manyan Labarai

Tsohon Kwamishina A Gombe, Ya Marawa Pantami Baya

September 13, 2026
Next Post
An Gudanar Da Taron Kirkire-Kirkire Na Duniya Na Kafafen Yada Labarai Karo Na Biyar

An Gudanar Da Taron Kirkire-Kirkire Na Duniya Na Kafafen Yada Labarai Karo Na Biyar

LABARAI MASU NASABA

Jawabin Xi A Taron BRICS, Mafita Ce Ga Matsalolin Duniya

Jawabin Xi A Taron BRICS, Mafita Ce Ga Matsalolin Duniya

September 14, 2026
Duk Wani Yunkuri Na Karfafa Burin Japan Na Fadada Karfin Soji Zai Jefa Yankin Cikin Hadari

Duk Wani Yunkuri Na Karfafa Burin Japan Na Fadada Karfin Soji Zai Jefa Yankin Cikin Hadari

September 14, 2026
Tsohon Firaminsitan Jordan: Kasar Sin Tana Kan Gaba Wajen Gudanar Da Fasahar AI A Duniya

Tsohon Firaminsitan Jordan: Kasar Sin Tana Kan Gaba Wajen Gudanar Da Fasahar AI A Duniya

September 14, 2026
Hadin Gwiwar BRICS Na Jagorantar Hadin Kan Kasashe Masu Tasowa Da Dogaro Da Karfin Kansu

Hadin Gwiwar BRICS Na Jagorantar Hadin Kan Kasashe Masu Tasowa Da Dogaro Da Karfin Kansu

September 14, 2026
Na Miƙa Kaina Ga Hukumomin Tsaro – Sanata Shehu Buba

Na Miƙa Kaina Ga Hukumomin Tsaro – Sanata Shehu Buba

September 14, 2026
Sin Na Shirin Fadada Samar Da Hidimomin Reno Da Na Kiwon Lafiyar Yara Masu Rahusa

Sin Na Shirin Fadada Samar Da Hidimomin Reno Da Na Kiwon Lafiyar Yara Masu Rahusa

September 14, 2026
Kogi

Babu Dalilin Da Zai Sa Nijeriya Yin Talauci – Obasanjo

September 14, 2026
Gudummawar Da Hada-Hadar Ba Da Hidima Ta Sin Take Kawo Wa Duniya

Gudummawar Da Hada-Hadar Ba Da Hidima Ta Sin Take Kawo Wa Duniya

September 14, 2026
Kogi

Air Peace Da United Nigeria, Jirage 2 Masu Latti Sosai Watan Agusta — NCAA

September 14, 2026
Ra’ayin Kasar Sin Kan Fasahar AI Yana Samar Da Damammaki Ga Afirka

Ra’ayin Kasar Sin Kan Fasahar AI Yana Samar Da Damammaki Ga Afirka

September 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.