An kashe shugaban jam’iyyar NDC na mazabar Fiidi, da ke ƙaramar hukumar Makurdi a Jihar Binuwai, Igbu Terhemen, bayan wasu da ake zargi da yan daba ne sun kai masa hari. An gano shi a sume a wani daji da ke kusa da gidansa, kafin daga bisani ya rasu.
Wani abokin marigayin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce Terhemen ya bar gidansa a yammacin Talata domin kallon wasan ƙwallon ƙafa a yankin Kanshio da ke Makurdi, amma bai dawo gida ba. Hakan ya sa ’yan uwa da abokansa suka fara neman sa.
Majiyar ta ce an gano Terhemen da misalin ƙarfe 2:00 na dare ranar Laraba a wani daji da ke kusa da gidansa, a yankin NNPC Depot, a kan titin Makurdi zuwa Otukpo. An garzaya da shi domin samun kulawar lafiya, amma ya rasu kafin ya samu magani. An kuma gano wayarsa tana tare da shi lokacin da aka kai gawarsa ɗakin ajiye gawa.
An kuma gano wata alama mai kama da raunin allura a jikinsa, lamarin da ya sa aka yi zargin cewa mai yiwuwa maharan sun yi masa allurar wani abu kafin su bar shi a dajin. Sai dai har yanzu ba a tabbatar da nau’in abin da ake zargin an yi masa allurar da shi ba. Jam’iyyar NDC ta Jihar Binuwai ta yi Allah-wadai da kisan, tana mai cewa an daure Terhemen da igiya tare da yi masa allurar wani abu da ake zargin mai guba ne.
Shugaban NDC na Jihar Binuwai, Ohini Ojegbe, ya yi kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da bincike domin gano wadanda suka aikata kisan tare da gurfanar da su a gaban kotu. Sai dai kakakin rundunar ’yansandan Jihar Binuwai, DSP Peter Aondongu, ya ce rundunar ba ta samu rahoton kisan ba a lokacin da aka tuntube ta.














