An gudanar da bikin musayar al’adu albarkacin cika shekaru 70 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Masar, a jiya Talata a birnin Alkahira na Masar, yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke gudanar da ziyarar aiki a kasar.
Kafar CMG ta kasar Sin da ma’aikatar watsa labarai ta Masar ne suka shirya bikin, kuma shugaban kasar Masar Abdel Fattah El-Sisi ya aike da sakon taya murnar gudanar da bikin, wanda ya hallara daruruwan baki daga bangaren siyasa, da tattalin arziki, da raya al’adu, da kwararru na kafofin watsa labarai daga Sin da Masar, wadanda kuma suka shaida gabatar da tarin nasarorin da aka cimma a fannin hadin gwiwar kafofin watsa labaran sassan biyu.
A jawabinsa yayin bikin, daraktan CMG Shen Haixiong, ya ce makala mai dauke da sa hannun shugaban kasar Sin Xi Jinping, wadda aka wallafa a kafofin kasar Masar, ta nuna aniyar Sin ta yin aiki tare da Masar ba tare da sauya ainihin manufar ba, kana an nuna shirin Sin na wanzar da yanayin da ya shude da bude kofa domin gaba, da goyon baya da ingiza matakan cimma nasarori da farfadowa, da hada hannu wajen samar da makoma mai haske ta bunkasa kasashen biyu, da ma dangantakar dake tsakaninsu.
Shen Haixiong, ya kara da cewa wannan biki mataki ne mai karko na aiwatar da kudurorin da shugabannin kasashen biyu suka cimma, kana zai zurfafa abota tsakanin Sin da Masar. (Saminu Alhassan)














