Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fara ziyarar aiki a Masar a jiya Talata, an kaddamar shirin “Bayanan Magabata da Xi Jinping yake So” na harshen Larabci, wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin (CMG) ya shirya, yayin wani taro da aka yi a birnin Alkahira na kasar Masar.
Shugaban Masar Abdel Fattah El-Sisi ya aike da sakon taya murnar gudanar da taron cikin nasara a daidai lokacin da Masar da Sin ke murnar cika shekaru 70 da kulla huldar diplomasiyya a tsakaninsu.
A cewar Abdel Fattah El-Sisi, shirin na gargajiya, kamar fassara bayanan magabata na Sinanci, ya gina wata gadar mu’amala tsakanin matasan Masar da na Sin.A nasa bangare, shugaban CMG Shen Haixiong, ya ce shekaru 70 da suka gabata, Masar ta kasance kasar Larabawa, kuma ta nahiyar Afrika ta farko da ta kulla huldar diplomasiyya da kasar Sin.
Kuma, karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu, dangantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Masar ta yi ta kai wa sabbin matsayi a shekarun baya-bayan nan.Ya ce shirin “Bayanan Magabata da Xi Jinping yake So” na harshen Larabci da CMG ya samar, ya bayyana hikimar siyasa ta shugaba Xi Jinping da ra’ayin falsafa da mahangarsa, wanda ya bude wata kafa ga daukacin al’umma, ta yaba wa hikimar shugaban wajen shugabantar kasar da tarin kyawawan damarmakin da Sin ke da su a sabon zamani, ta yadda za su kyautata fahimtarsu game da al’adu da hikima da ruhin kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)














