An binne tsohon gwamnan tsohuwar jihar Gongola, Alhaji Bamanga Tukur, a birnin Yola ta jihar Adamawa ranar Lahadi 13/9/2026.
Babban Limamin Masallacin Juma’a na Modibbo Adama, Imam Khadi Ahmadu Bobboi, ne ya jagoranci sallar jana’izar marigayin, wanda aka kai shi zuwa makwancinsa na karshe.
An gudanar da sallar jana’izar ne a fadar mai martaba Lamido Adamawa Dakta Muhammadu Barkindo Aliyu Mustapha, inda Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Rt. Hon. Bathiya Wesley, da tsohon gwamna Umaru Bindow Jibrilla, da hamshakin ɗan kasuwa Aliko Dangote, da sauran manyan mutane suka halarta.
Ana dai ta bayyana saƙonni na girmamawa da ta’aziyya daga waɗanda suka halarci sallar jana’izar da jama’a daidaiku.














