Ministan kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire na Afirka ta Kudu, Blade Nzimande, ya yi kira da a kara karfafa hadin gwiwa na kut-da-kut a fannin kimiyya da fasaha tare da kasar Sin, inda ya bayyana cewa wannan hadin gwiwa wani muhimmin bangare ne na dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.
Nzimande ya yi wannan tsokaci ne a taron dandalin kirkire-kirkire na Pujiang na shekarar 2026 da aka gudanar a birnin Shanghai na kasar Sin, jiya Asabar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Afirka ta Kudu ya ruwaito.Ya ce Afirka ta Kudu da Sin, za su ci gaba da kulla hadin gwiwa na kut-da-kut a fannonin fasahar kirkirarriyar basira, da cibiyoyin bincike na hadin gwiwa, da kimiyyar sararin samaniya da ilimin taurari na duniyoyi, da fasahar kwantum mai nazarin ayyukan kwayoyin zarra, da tsaron sadarwar intanet, da ci gaban matasa da sauransu.
Nzimande ya ce, Afirka ta Kudu a shirye take ta yi aiki tare da kasar Sin da sauran abokan hadin gwiwa, don samar da wata makoma da za a rika bayar da sabbin kirkire-kirkire ga saura, da yin amfani da fasaha ta hanyar da ta dace, kuma kimiyya ta zama wata gada tsakanin kasashe, da al’ummomi da kuma zuriyoyi.Wanda aka kaddamar a shekarar 2008, dandalin sabbin kirkire-kirkire na Pujiang, wani taro ne na shekara-shekara da ma’aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Sin da gwamnatin birnin Shanghai suke shiryawa. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)













