An gudanar da taro na 3, na kwamitin hadin gwiwa na kasashen Sin da Iran da Saudiyya, yau Talata, a birnin Tehran na Iran, domin bibiyar yadda ake aiwatar da yarjejeniyar nan ta Beijing.
Kasashen Iran da Saudiyya sun sake nanata kudurinsu na biyayya ga tanade tanaden yarjejeniyar da ci gaba da karfafa dangantakar abota da makwabtaka dake tsakaninsu. Sun kuma ce maraba da karin gudunmuwar Sin, kuma sun yi imanin cewa, abu ne mai muhimmanci ga Sin ta goyi bayan yarjejeniyar tare da bibiyar yadda ake aiwatar da ita.
A nata bangare, kasar Sin ta yi bayyana kudurinta na ci gaba da marawa Iran da Saudiyya baya, da kuma karfafa musu gwiwar daukar matakan raya huldarsu a bangarori da dama. (Mai fassara: FMM)














