Yau Talata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian ya jagoranci taron manema labarai na yau da kullum. Yayin taron, wani dan jarida ya yi tambaya game da karin takunkumin da Amurka ta kakaba wa Iran. Inda Lin Jian ya bayyana cewa, Sin ta sha nuna adawarta ga takunkumin da ba ya bisa ka’ida wanda ba shi da tushe a cikin dokokin kasa da kasa kuma ba shi da iznin kwamitin sulhu na MDD.
Ya ce hadin gwiwa tsakanin Sin da Iran na ci gaba da tafiya karkashin tsarin dokokin kasa da kasa kuma bai kamata a lalata shi ba. Yana cewa Sin tana sa ido sosai kan lamarin kuma za ta dauki duk matakan da suka dace don kare halaltattun hakkoki da muradunta.
Bugu da kari, game da ci gaban harkokin kimiyya da fasaha na Sin, Lin Jian ya ce tushen manufar da ke haifar da habaka kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha ta Sin shi ne bude kofa don hadin gwiwa, da cimma moriyar juna da samun nasara tare.
Ya ce a shirye Sin take ta yi aiki tare da kasashen duniya don ci gaba da tattaunawa da hadin gwiwa a fannonin fasahohin zamani kamar fasahohin AI.(Safiyah Ma)














