ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 16, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Kaddamar Da Taron Dandalin Tattauna Hadin Gwiwar Fasahohi Da Masana’antun Aikin Gona na Sin Da Afirka A Kenya

by Sulaiman
3 months ago
Kenya

A jiya Talata ne aka bude taron dandalin tattauna hadin gwiwar fasahohi da masana’antun aikin gona na Sin da Afirka na kwanaki 3 a birnin Nairobin kasar Kenya. A yayin taron, wakilai sama da 100 daga hukumomin gwamnatin Sin da na kasashen Afirka, da kungiyoyin kasa da kasa, da cibiyoyin nazarin kimiyya da fasaha, da manyan makarantu, da kungiyoyin kasuwanci, da kuma kamfanoni da dama, sun yi tattaunawa mai zurfi kan sabuwar hanyar habaka hadin gwiwar Sin da Afirka, a fannin neman zamanintar da aikin gona cikin hadin gwiwa.

Jakadiyar kasar Sin dake kasar Kenya, Guo Haiyan ta gabatar da jawabi a yayin bikin kaddamar da taron, inda ta ce bisa tsarin taron dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC, zamanintar da aikin gona ya kasance muhimmin bangare a hadin gwiwar Sin da Afirka domin cimma moriyar juna.

Kasashen Afirka na da albarkatun kasa da matasa masu yawa, kuma idan har aka hade fasahohin neman ci gaba na kasar Sin, da fasahohin aikin gona na zamani, da kuma manyan kasuwanni na kasar Sin, tabbas za su bayar da muhimmiyar gudummawa a fannin gaggauta zamanintarwar aikin gona, da daga matsayin samar da isasshen hatsi, da neman wadata tare a kasar Sin da kasashen Afirka.

ADVERTISEMENT

A nasa tsokaci kuwa, mataimakin shugaban shirin raya noma ta hanyar jure sauyin yanayi na Afirka ko AGRA mista Hamadi Boga, ya bayyana cewa, hadin gwiwar aikin gona zai samar da damammaki ga kasar Sin da kasashen Afirka wajen kafa tsarin samar da isasshen hatsi mai inganci, da samar da guraben aikin yi tare da kuma samun wadata tare.

An gudanar da taron na wannan karo ne karkashin hadin gwiwar cibiyar kirkire-kirkiren kimiyya da fasahar aikin gona ta Jingwa, da kwalejin nazarin tattalin arziki da manufofin abinci ta duniya dake jami’ar aikin gona ta kasar Sin, da kawancen shirin AGRA, da kuma taron kirkire-kirkiren kimiyya da fasahar aikin gona na duniya da dai sauransu. (Mai Fassara: Maryam Yang)

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Fitar Da Ka’idojin Na’urar Kiwon Lafiya Ta Sadarwa Tsakanin Kwakwalwa Da Na’ura Mai Amfani Da AI

Rokar Gravity-1 Na Kasar Sin Ya Harba Sabbin Taurarin Dan’adam Daga Teku

Kenya
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sin Ta Fitar Da Ka’idojin Na’urar Kiwon Lafiya Ta Sadarwa Tsakanin Kwakwalwa Da Na’ura Mai Amfani Da AI
  • Sulaiman
    Gwamnan Kano Ya Naɗa Hafsat Kutama Mukaddashiyar Shugabar Hukumar PCACC 
  • Sulaiman
    Rokar Gravity-1 Na Kasar Sin Ya Harba Sabbin Taurarin Dan’adam Daga Teku
  • Sulaiman
    Xi Ya Taya Jami’ar Jilin Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

MASU ALAKA

Sin Ta Fitar Da Ka’idojin Na’urar Kiwon Lafiya Ta Sadarwa Tsakanin Kwakwalwa Da Na’ura Mai Amfani Da AI
Daga Birnin Sin

Sin Ta Fitar Da Ka’idojin Na’urar Kiwon Lafiya Ta Sadarwa Tsakanin Kwakwalwa Da Na’ura Mai Amfani Da AI

September 16, 2026

Next Post
Auren Gata: Babu Saki Sai Da Amincewar Hisbah – Daurawa

TCN Ta Samar Da Hanyar Samun Wutar Lantarki A Kebbi Ta Wucin Gadi

TCN Ta Samar Da Hanyar Samun Wutar Lantarki A Kebbi Ta Wucin Gadi

September 16, 2026
APC Ta Tsawaita Rijistar Mambobinta, Ta Ɗage Ranar Babban Taronta Na Ƙasa

APC Ta Nemi A Gudanar Da Bincike Kan Farmakin Da A Kai Ofisoshinta A Kaduna

September 16, 2026
2023: Me Ya Sa Ake Rububin Wike?

Ban Taɓa Yi Wa Tinubu Alƙawarin Zan Koma APC Ba – Wike

September 16, 2026
Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda Sama Da 1,100 Cikin Shekara Ɗaya – Kwamanda

Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda Sama Da 1,100 Cikin Shekara Ɗaya – Kwamanda

September 16, 2026
Tinubu Zai Kayar Da Atiku Da Obi Ko Da Sun Haɗa Kai – Fayose

Tinubu Zai Kayar Da Atiku Da Obi Ko Da Sun Haɗa Kai – Fayose

September 16, 2026
Jarumin Nollywood Olu Jacobs Ya Rasu Yana Da Shekaru 84

Jarumin Nollywood Olu Jacobs Ya Rasu Yana Da Shekaru 84

September 16, 2026
Xi Ya Taya Jami’ar Jilin Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

Xi Ya Taya Jami’ar Jilin Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

September 16, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.