ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, July 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Kama Tsohon Minista Uche Nnaji Kan Zargin Amfani Da Takardun Bogi

by Sadiq
3 weeks ago

An kama tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, a Filin Jirgin Saman Akanu Ibiam da ke Enugu.

Jaridar Premium Times ta ruwaito ce an kama Nnaji ne da safiyar ranar Laraba yayin da yake shirin zuwa Abuja.

Ana sa ran za a miƙa shi ga Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) domin ci gaba da bincike.

ADVERTISEMENT

An kama shi ne bayan wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bai wa ICPC umarnin kama shi a watan Yuni bisa zargin gabatar da takardun shaidar karatu na ƙarya.

Kotun ta kuma bai wa hukumar izinin ayyana shi a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo idan ya ƙi amsa gayyata.

LABARAI MASU NASABA

Sana’ar Kilishi:Yadda Ta Bunkasa Daga Jihar Katsina Zuwa Wasu Sassan Nijeriya

Batun Yawan Bashin Da Nijeriya Ke Ciyowa Daga Ketare

ICPC ta shaida wa kotun cewa Nnaji ya yi watsi da gayyatar da aka yi masa domin amsa tambayoyi kan zargin.

Ana zargin Nnaji da gabatar da takardun digiri na Jami’ar Nsukka (UNN) da kuma takardar kammala NYSC na ƙarya lokacin da aka naɗa shi minista a shekarar 2023.

Nnaji ya yi murabus daga muƙaminsa a watan Oktoban 2025, inda ya ce ya sauka ne domin bin doka da ƙa’ida, ba wai saboda ya amince da zargin da ake masa ba.

Kafin a kama shi, Nnaji ya musanta zargin tare da ƙalubalantar umarnin kotun a Kotun Ɗaukaka Ƙara.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga Nnaji ko kuma ICPC kan kama shi.

MASU ALAKA

Sana’ar Kilishi:Yadda Ta Bunkasa Daga Jihar Katsina Zuwa Wasu Sassan Nijeriya
Manyan Labarai

Sana’ar Kilishi:Yadda Ta Bunkasa Daga Jihar Katsina Zuwa Wasu Sassan Nijeriya

July 24, 2026
Batun Yawan Bashin Da Nijeriya Ke Ciyowa Daga Ketare
Manyan Labarai

Batun Yawan Bashin Da Nijeriya Ke Ciyowa Daga Ketare

July 24, 2026
Wasikar Trump Ba Za Ta Taimaki Tinubu Ya Lashe Zaɓen 2027 Ba – ADC
Manyan Labarai

Wasikar Trump Ba Za Ta Taimaki Tinubu Ya Lashe Zaɓen 2027 Ba – ADC

July 23, 2026
Next Post
Kasar Sin Za Ta Nace Ga Fadada Bude Kofarta Ga Kasashen Waje

Kasar Sin Za Ta Nace Ga Fadada Bude Kofarta Ga Kasashen Waje

LABARAI MASU NASABA

Jadawalin INEC:Kotun Daukaka Kara Ta Kassara Fatan Jam’iyyu Da ‘Yan Siyasa

Jadawalin INEC:Kotun Daukaka Kara Ta Kassara Fatan Jam’iyyu Da ‘Yan Siyasa

July 24, 2026
An Zartas Da Sanarwar Chengdu A Taron Ministocin Kungiyar APEC Kan Harkar Raya Fasahohin Dijital Da AI

An Zartas Da Sanarwar Chengdu A Taron Ministocin Kungiyar APEC Kan Harkar Raya Fasahohin Dijital Da AI

July 24, 2026
NNPP Za Ta Kwace Mulki A Jihar Imo – Kwankwaso

Jam’iyyar NDC Ta Shirya Tsaf Domin Kafa Gwamnati A 2027 —Kwankwaso

July 24, 2026
Sin Ta Kara Kamfanoni 14 Na Tarayyar Turai Cikin Jerin Wadanda Aka Hana Fitar Masu Da Kaya

Sin Ta Kara Kamfanoni 14 Na Tarayyar Turai Cikin Jerin Wadanda Aka Hana Fitar Masu Da Kaya

July 24, 2026
Kashim Shettima Ya Mayar Da Martani Kan Tsadar Rayuwa

Kyamar Baki: Shettima Ya Ja Kunnen Gwamnatin Afirka Ta Kudu

July 24, 2026
Yadda Kasar Sin Ta Samar Da Ci Gaba Na Bai Daya

Yadda Kasar Sin Ta Samar Da Ci Gaba Na Bai Daya

July 24, 2026
Hatsin Da Kasar Sin Ta Girbe Da Lokacin Zafin Bana Ya Zarce Tan Miliyan 150

Hatsin Da Kasar Sin Ta Girbe Da Lokacin Zafin Bana Ya Zarce Tan Miliyan 150

July 24, 2026
Wani Dalilin Da Ya Sa Al’Ummar Afirka Ke Kaunar Kasar Sin Shi Ne Yadda Take Kokarin Zuba Musu Jari

Wani Dalilin Da Ya Sa Al’Ummar Afirka Ke Kaunar Kasar Sin Shi Ne Yadda Take Kokarin Zuba Musu Jari

July 24, 2026
NLC Ta Yi Barazanar Daukar Matakin Yajin Aiki Kan Albashi Mafi Karanci

NLC Ta Yi Barazanar Daukar Matakin Yajin Aiki Kan Albashi Mafi Karanci

July 24, 2026
Sin Tana Son More Damammakin Fasahar AI a Maimakon Babakere a Wannan Bangare Da Kasashen Yamma Suka Dade Suna Yi

Sin Tana Son More Damammakin Fasahar AI a Maimakon Babakere a Wannan Bangare Da Kasashen Yamma Suka Dade Suna Yi

July 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.