An bude taron dandalin manyan jami’an kafafen watsa labarai na yankin Asiya da Pacific a yau 5 ga watan nan a birnin Shenzhen na kasar Sin. Li Shulei, mamba na ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS) kuma shugaban sashen yada labarai na kwamitin tsakiya na JKS, ya halarci bikin bude taron kuma ya gabatar da muhimmin jawabi.
Kazalika, Huang Kunming, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya kuma sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminis na lardin Guangdong, shi ma ya halarta tare da gabatar da jawabi.Mahalarta taron sun bayyana cewa, ba za a iya raba samun ci gaba da hadin gwiwa a yankin Asiya da Pacific da shigar kafafen watsa labarai na yankin a dama da su ba.
Sun jaddada bukatar zurfafa hadin gwiwa a fagage kamar bayar da rahoto na hadin gwiwa, da sabbin kirkire-kirkire na fasaha, da kuma samar da hazikai, ta hanyar amfani da musayar kafafen watsa labarai domin gadar da wayewa, da yada al’adu, da kuma sada zumunta.
Taron dandalin mai taken “Gina Al’ummar Yankin Asiya da Pacific Mai Wadata: Cimma Matsayar Kafafen Watsa Labarai da Daukar Mataki,” ya samu halartar wakilai sama da 400 daga kasashe da yankuna fiye da 40, da Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin kasa da kasa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














