ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, September 8, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

by Leadership Hausa
3 days ago
Zabe

Tsoma bakin kasashen waje a zaben Nijeriya ba sabon abu bane. Kafin zaben ranar 12 ga Yuni, an ji labarin cewa marigayi shugaban Libiyya, Muammar Gaddafi ya bayar da babban gudummawar kudi ga wasu ‘yan takara.

A shekarar 2015, tsohon shugaban kasa, Goodluck ya zargi John Kerry, wanda shi ne sakataren harkokin wajen Amurka a wancen lokaci, da yin wani shiri na kasashen yamma na kokarin raunana tazarcensa.

Haka kuma a shekarar 2023, Shugaban kasa, Bola Tinubu, wanda a wancan lokacin dan takara ne kawai, da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar sun yi kokarin samun neman goyon baya daga gwamnatin Joe Biden.

ADVERTISEMENT

A shekarar 2027, shugabannin kasashen waje sun zuba idanu kan zaben Nijeriya, ciki har da Romauld Wadagni, Faure Gnassingbe, Omar Tchiani, Mohamed Bazoum, Assimi Goita, Ibrahim Traore, Mahamat Deby, har ma da kasashen yamma da ke fafatawa don samun tasiri a yammacin Afirka.

Dokar kasa ta dora wa hukumar leken asirin kasa (NIA) alhakin sa ido kan ayyukan wakilai da ma’aikatan kasashen waje.

LABARAI MASU NASABA

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki

Yayin da zaben ke karatowa, NIA da daraktanta, Mohammed Mohammed, na iya samun ayyuka da yawa da jerin kasashen da suke ganin suna da hannu a sakamakon zaben.

Moahemmed da kansa ba sabon abu bane a gareshi wajen yin aikin a kasashen da ke gudanar da kamfen din tasiri kan makwabtansu, kamar Koriya ta Arewa, Pakistan, da Libiya a karkashin shugabancin Gaddafi.

Amma yana fuskantar kalubale daban da na wadanda suka gabace shi, Yammacin Afirka ya sha bamban da matakin kashin kai da kuma kwarewa na aiki.

Uche Okeke ya yi kokari wajen kafa kwamitin leken asiri na harkokin tsaron Afirka. Olaniyi Oladeji ya shafe lokaci a Benin, shi kuma Ahmed Abubakar ya kwashe wani bangare na rayuwarsa a Chadi. Mohammed yana fuskantar yankin da aka karkasa.

A lokacin da tsohon shugaban rudunar sojojin Nijeriya, Tukur Bururai ya nuna yuwuwar katsalandar daga kasashen waje, babu wani shaida da ke nuna cewa makwabtan Nijeriya na kokarin yin tasiri a sakamakon zaben 2027.

Amma wasu suna matsayin abokan hulda na Rasha, kuma ba asirirce ba ne cewa wasu daga cikinsu suna da boyayyun fatan samun sauyi a siyasa.

Duk da haka, tsoma baki a zabe na iya bayyana ta hanyoyi kamar gudanar da kamfen a kafafen sada zumunta ta amfani da wakilan da aka biya, kutse cikin tsarin da ba shi da karfi, da kuma gina goyon baya ko adawa da ‘yan takara ta hanyar diflomasiyya.

A aikaice, Shugaba Tinubu ya kuma saka kansa cikin tsarin dimokuradiyya na kasashen makwabta kamar Nijar, Benin, Mali, da Burkina Faso.

A kasar Benin, Romuald Wadagni ba zai kasance shugaba a yau ba idan ba don Shugaba Tinubu ba. Duk da haka, tattalin arzikin kasa, kamar na Togo, ya sha tasiri ga manufofin gwamnatin Tinubu.

Masana’antar motoci ta Tokunbo a Benin, wacce take samun gagarumin tasiri daga Nijeriya, ta rushe. Hada kasuwar harkokin caji ya kuma sa kayayyaki da ayyuka sun yi arha a Nijeriya, wanda ya sa dole Benin ta rage abin da za ta fitar zuwa makwabciyarta.

Shugabannin kasashen Sahel na da korafe-korafe mafi girma fiye da tattalin arzikinsu. Rashin jin dadinsu ya juyawa zuwa zaman lafiyar siyasa da tsaro, kafuwar mulkin soja, da kuma kawo karshen tasirin mulkin mallaka.

Zabe
Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja
  • Leadership Hausa
    Batun Dawo Da Tallafin Mai Da Atiku Ya Yi Na Ci Gaba Da Tayar Da Kura
  • Leadership Hausa
    Batun Guguwar Kakar Yakin Neman Zabukan 2027 A Nijeriya
  • Leadership Hausa
    Batun Hare-haren Ƴan Bindiga A Wasu Ƙauyukan Kaduna

MASU ALAKA

Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Umarnin Kawo Karshen Matsalar Tsaro
Rahotonni

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

September 5, 2026
Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
Rahotonni

Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki

September 5, 2026
Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
Rahotonni

Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye

September 5, 2026
Next Post
Jami’in Xigaze: Ana Iyakacin Kokari Wajen Neman Mutanen Da Suka Bace

Jami’in Xigaze: Ana Iyakacin Kokari Wajen Neman Mutanen Da Suka Bace

LABARAI MASU NASABA

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026
Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

September 8, 2026
Ballon D'or

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.