ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Yi Taron Kara Wa Juna Sani Game Da Hadin-Gwiwar Sin Da Afirka A Fannin Tabbatar Da Tsaro A Kasar Habasha

by Sulaiman
9 months ago
Sin

LABARAI MASU NASABA

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

An yi wani taron kara wa juna sani na kasa da kasa mai taken “Tabbatar da tsaro cikin hadin-gwiwa: Sin da Afirka na daukar matakai tare”, jiya Alhamis 4 ga watan Disamba a hedikwatar kungiyar tarayyar Afirka wato AU da ke Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha. Taron ya samu halartar jami’an diflomasiyya na kasa da kasa, gami da wakilan AU da Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kwararru da kafafen yada labarai na kasashe daban-daban.

Shugabar sashin kula da harkokin tsaro na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Wang Lixin ta gabatar da jawabi cewa, duniya na fuskantar yanayi mai sarkakiya a halin yanzu, inda kokarin kasar Sin na aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 15 ke haifar da manyan damarmaki ga duk duniya. Ta ce ya dace Sin da Afirka su kara hada kai don aiwatar da shawarar tabbatar da tsaro a duniya, da shawarar inganta tsarin shugabancin duniya, da taimakawa ga zamanantar da harkokin zaman lafiya da tsaro, da kyautata tsarin shugabancin duniya, da kara raya al’ummomin Sin da Afirka masu kyakkyawar makoma ta bai daya, da zummar bayar da karin gudummawa ga sha’anin wanzar da zaman lafiya da samar da ci gaba a duniya.

A nasa bangaren kuwa, mataimakin darektan ofishin shugaban kwamitin kungiyar AU, Moussa Mohamed Omar ya bayyana cewa, matsalolin tsaro da nahiyar Afirka ke fuskanta yanzu, ba matsaloli ne da ke shafar wannan shiyya kawai ba, ciki har da ta’addanci, da yaduwar makamai ta hanyar da ba ta dace ba, da kuma sauyin yanayi. Shawarar inganta tsaro ta duniya na tsayawa kan aiwatar da ra’ayin tsaro mai dorewa kuma cikin hadin-gwiwa, al’amarin da ya dace da matsayar Afirka.

ADVERTISEMENT

Tawagar jami’an diflomasiyyar kasar Sin da ke AU, da kwamitin AU, gami da ofishin MDD da ke AU din, su ne suka dauki nauyin shirya taron, inda mahalarta ke ganin cewa, shawarar kasar Sin ta bullo da dabarun kasar a fannin shawo kan kalubalen da Afirka, har ma da duk duniya ke fuskanta, kana, kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa ga tabbatar da tsaro da samar da ci gaba a Afirka, kuma karfafa hadin-gwiwar Sin da Afirka zai kara sanya kuzari ga duk duniya. (Murtala Zhang)

Sin
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen
  • Sulaiman
    Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci
  • Sulaiman
    Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

MASU ALAKA

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen
Daga Birnin Sin

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026

September 9, 2026
Next Post
Sin

Ranar Ƙanjamau Ta Duniya: Remi Tinubu Ta Nemi Matasa Su Rungumi Aƙidar Gwaji

LABARAI MASU NASABA

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026
Sin

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
Sin

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.