ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

’Yansanda Sun Kama Wani Mutum da Harsasai 174 A Nasarawa

by Sadiq
3 months ago

Rundunar ’Yansandan Jihar Nasarawa ta kama wani mutum da harsasai guda 174 na AK-47 a hanyar Toto zuwa Abaji.

An kama wanda ake zargin, mai suna Abubakar Abdullahi, ne a ranar Lahadi, 22 ga Yuni, 2026, lokacin da jami’an ’yansandan yankin Toto suke sintiri.

ADVERTISEMENT

’Yansanda sun ce bayan sun bincike shi, sun gano harsasai 174 da ya ɓoye a jikinsa.

Kakakin rundunar ’yansandan jihar, SP Ramhan Nansel, ya ce wanda aka kama ya kasa bayyana daga ina ya samo harsasan, waye mai su, ko kuma inda yake kai su.

LABARAI MASU NASABA

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

’Yansanda sun fara bincike domin gano ko akwai wasu mutane da ke da hannu a lamarin ko wata ƙungiyar masu aikata laifi da ka iya kasancewa tana da alaƙa da safarar harsasan.

Kwamishinan ’Yansandan Jihar Nasarawa, Shetima Jauro Mohammed, ya ce rundunar ta himmatu wajen yaƙi da aikata laifuka da kuma hana yaɗuwar makamai ba bisa ƙa’ida ba a jihar.

Ya gargaɗi masu aikata laifuka cewa ba za a ba su mafaka a jihar ba, yana mai cewa ’yansanda za su ci gaba da gudanar da ayyukan leƙen asiri, sa ido da sauran matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Rundunar ta kuma buƙaci jama’a da su riƙa bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai da za su taimaka wajen yaƙi da laifuka da tabbatar da zaman lafiya a jihar.

MASU ALAKA

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro
Manyan Labarai

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

September 11, 2026
Manyan Labarai

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

September 11, 2026
Manyan Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

September 11, 2026
Next Post
Trump Ne Zai Jagoranci Bayar Da Kofin Duniya A Wasan Ƙarshe – Infantino

Trump Ne Zai Jagoranci Bayar Da Kofin Duniya A Wasan Ƙarshe – Infantino

LABARAI MASU NASABA

Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

September 11, 2026
Zaben 2027: Jam’iyyun Siyasa Sun Bayyana Shirinsu Yayin Da INEC Ta Fitar Da Jawalin Zabe

Dalilan Da Ya Sa Jam’iyyun Siyasa Suka Jinkirta Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen

September 11, 2026
Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

September 11, 2026
Za A Ci ’Yan Siyasa Masu Kalaman Ɓatanci Tarar Miliyan 10 Da Ɗaurin Watanni 12 — INEC

2027: A Karon Farko INEC Za Ta Ƙaddamar Da Na’urar Bibiyar Zaɓen Nijeriya

September 11, 2026
Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

September 11, 2026
Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026  Mrs Zubaida Umar

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026 Mrs Zubaida Umar

September 11, 2026
Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

September 11, 2026
Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

September 11, 2026
Sanata yari

Gwarzon Ɗan Siyasa Na Shekarar 2026 Sanata Abdul’Aziz Abubakar Yari

September 11, 2026
Kasar Sin Za Ta Taimaka Wajen Bunkasa Wadatar Makamashi Da Ci Gaba Mai Dorewa A Duniya

Kasar Sin Za Ta Taimaka Wajen Bunkasa Wadatar Makamashi Da Ci Gaba Mai Dorewa A Duniya

September 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.