ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Atiku Ya Soki Tsare El-Rufai, Ya Ce Sharuɗan Belinsa Sun Yi Tsauri

by Sadiq
3 months ago

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, , ya nuna damuwa kan ci gaba da tsare tsohon gwamnan Jihar Kaduna, yana mai cewa sharuɗan beli bai kamata su zama hanyar hukunta mutum kafin kotu ta yanke hukunci a kansa ba.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, Atiku ya ce beli na da muhimmanci wajen kare haƙƙin wanda ake tuhuma, domin doka ta ɗauki mutum a matsayin marar laifi har sai an tabbatar da laifinsa a kotu.

Ya yi tambaya kan sharuɗan belin da aka gindaya wa El-Rufai, waɗanda suka haɗa da gabatar da wani ma’aikacin gwamnatin tarayya mai matsayi na 17 da ke aiki a halin yanzu, wanda kuma yake da gida a Maitama ko Asokoro a Abuja, tare da wasu ƙarin sharuɗa.

ADVERTISEMENT

A cewarsa, irin waɗannan sharuɗa suna da wahalar cikawa ga yawancin ’yan Nijeriya, kuma suna haifar da tambaya ko da gaske an yi niyyar bayar da beli ne ko kuma hana wanda ake tuhuma.

Atiku ya ce batun ba iya El-Rufai kaɗai ya shafa ba domin yana da tasiri ga duk wani ɗan ƙasa da zai iya fuskantar irin wannan hali a gaba.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ya jaddada cewa ya kamata tsarin shari’a ya kasance mai adalci da sauƙin samu ga kowa, ba tare da la’akari da matsayinsa ko ra’ayinsa na siyasa ba.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma ce aikin kotu shi ne tabbatar da adalci da kare ’yancin jama’a, ba wai amfani da sharuɗan beli wajen ci gaba da tsare mutum ba.

Ya yi gargaɗin cewa idan sharuɗan beli suka zama kasance ba za a iya cikawa ba, hakan na nufin an hana mutum samun beli, wanda zai iya tauye haƙƙoƙin da kundin tsarin mulki ya tanada.

Atiku ya yi kira ga ɓangaren shari’a da ya ci gaba da kare ’yancin jama’a, tabbatar da adalci da kuma mutunta doka domin ƙarfafa dimokuraɗiyya a Nijeriya.

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
Next Post
Xi Ya Yi Kiran Daukar Matakan Zamanantar Da Aikin Gona Da Yankunan Karkara

Xi Ya Yi Kiran Daukar Matakan Zamanantar Da Aikin Gona Da Yankunan Karkara

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.