ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ranar Ƙanjamau Ta Duniya: Remi Tinubu Ta Nemi Matasa Su Rungumi Aƙidar Gwaji

by Sani Anwar
9 months ago
Duniya

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Remi Tinubu, ta yi kira ga matasan Nijeriya da su ɗauki nauyin kula da lafiyarsu ta hanyar yin gwajin cutar ƙanjamau da kuma neman magani, yayin da duniya ke bikin ranar yaƙi da cutar ta ƙanjamau ta 2025.

A cikin wani saƙo da ta fitar a ranar Litinin, Uwargidan Shugaban Ƙasar ta ce; taken na bana shi ne, “Mayar Da Hankali Tare Da Magance Cutar Ƙanjamau,” ya ba da dama ga ƙasar ta hanyar sabunta alƙawarinta na kawo ƙarshen cutar ƙanjamau nan da shekara ta 2030.

Har ila yau, ta yi nuni da cewa; duk da cewa, Nijeriya ta samu ci gaba sosai a fannin rigakafin cutar ƙanjamau da jiyya da kuma kulawa a tsawon shekaru, amma duk da haka akwai buƙatar ƙara yin aiki tuƙuru, don tabbatar da cewa; kowane ɗan ƙasa ya samu damar yin ayyukan ceton rai, ba tare da tsoro ko wariya ba.

ADVERTISEMENT
  • Duniya Za Ta Kara Kyau In Ba A Nuna Fin Karfi
  • Sin Na Kokarin Yin Kirkire-kirkire Don Sa Kaimi Ga Samun Moriyar Juna A Duniya

“Kowane ɗan Nijeriya ya cancanci samun damar ceto rai, ba tare da ƙyama ko nuna wariya ba,” in ji ta.

Sanata Tinubu ta buƙaci matasa a faɗin ƙasar nan da su ba da fifiko wajen yin gwaje-gwaje a-kai-a-kai tare da sanar da su game da cutar ƙanjamau.

LABARAI MASU NASABA

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Har ila yau, ta nanata cewa; gano cutar da wuri da kuma yin magani a kan lokaci na da matuƙar muhimmanci wajen cimma cutar ta ƙanjamau (AIDS).

“Ina kira ga matasanmu, ku kula da lafiyarku, ku san illar cutar HIƁ ta hanyar yin gwaji, sannan kuma ku nemi magani da zarar kun kamu da ita,” in ji ta.

Haka zalika, Uwargidan Shugaban Ƙasar ta yi kira ga iyalai, masu kulawa da unguwanni da su nuna tausayi tare da bayar da tallafi ga waɗanda ke ɗauke da cutar ta ƙanjamau.

Sannan ta sake nanata cewa, ƙyama na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke kawo cikas ga ci gaba a matakin yaƙi da cutar ta ƙanjamau a faɗin wannan ƙasa, kazalika kuma dole ne a fuskanci juna ta hanyar kawar da wannan ƙyama a tsakanin al’umma.

“Saboda haka, ina kira ga al’umma da ku nuna tausayi da goyon baya tare da kawar da ƙyama a tsakanin masu ɗauke da cutar,” in ji ta.

Sanata Tinubu ta jaddada aniyar gwamnatin tarayya na ƙara ƙaimi ga ƙoƙarin da ƙasa ke yi na kawo ƙarshen cutar ƙanjamau a matsayin barazana ga lafiyar jama’a nan da shekara ta 2030, wanda hakan ya yi daidai da manufofin duniya da Majalisar Ɗinkin Duniya da abokan aikin lafiya na duniya ke jagoranta.

Har wa yau, ta ƙarƙare da miƙa fatan alheri ga ɗaukacin ƴan Nijeriya, tana mai cewa, “Barka da ranar Ƙanjamau ta duniya (2025).”

Duniya
Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta

MASU ALAKA

Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato
Manyan Labarai

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia
Manyan Labarai

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato
Manyan Labarai

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Next Post
Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Sabon Tsarin Ci Gaban Zamfara Na Shekaru 10

Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Sabon Tsarin Ci Gaban Zamfara Na Shekaru 10

LABARAI MASU NASABA

Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.