Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya soki gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan yadda ta tafiyar da cire tallafin man fetur, yana mai cewa matakin ya ƙara tsananta tsadar rayuwa a Nijeriya.
Atiku ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Babban Mataimakinsa na Musamman kan Sadarwa da Jama’a, Phrank Shaibu, ya fitar.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce tashin farashin man fetur, taki da siminti na daga cikin abubuwan da ke nuna irin matsin tattalin arzikin da ’yan Nijeriya ke fuskanta.
A cewarsa, farashin taki ya tashi daga kusan Naira 9,000 zuwa Naira 50,000, yayin da farashin litar man fetur ya ƙaru daga Naira 199 zuwa kusan Naira 1,400.
Ya ƙara da cewa farashin buhun siminti ya tashi daga kusan Naira 4,000 zuwa Naira 13,500.
Atiku ya kuma yi nuni da cewa darajar Naira ta samu sauyi sosai a kasuwar canjin kuɗi, inda ya ce dala ta tashi daga kusan Naira 450 zuwa Naira 1,400.
Ya ce wannan ƙarin farashin ya shafi rayuwar ’yan Najeriya kai tsaye, musamman ta fuskar sufuri da kayan abinci.
Atiku ya bayyana cewa cire tallafin man fetur ya haifar da ƙarin farashin man fetur, sufuri da abinci, lamarin da ya ƙara wa ’yan Nijeriya nauyin rayuwa.
Ya kuma soki Shugaba Tinubu kan adawa da shawarar da ya gabatar ta samar da tallafin samarwa, wanda ya ce zai taimaka wajen rage farashin kayayyaki da kuma sauƙaƙa wa masu amfani da su.
Sai dai Atiku ya jaddada cewa ya kamata a samar da matakan tattalin arziki da za su rage wa ’yan Nijeriya raɗaɗin tsadar rayuwa tare da farfaɗo da harkokin samar da kayayyaki a ƙasar.














