Tawagar mata ‘yan kasa da shekaru 20 na Nijeriya (Super Falconets) za su fara gasar cin kofin Duniya ta mata ta FIFA ta ‘yan kasa da shekara 20 da kasar Spain a yau Litinin.
Kocin tawagar, Moses Aduku ya bayyana hakan, inda ya ce, a shirye tawagarshi take domin tunkarar Spain din ba tare da fargaba ko tsoro ba.
An shirya gudanar da fafatawar ta rukunin F da karfe 4 na yamma agogon Nijeriya a filin wasa na Sosnowiec na kasar Poland. Sau biyu tawagar ta Falconets ke karewa a matsayi na biyu na gasar a tarihi, inda suka zo a matsayi na biyu a shekarun 2010 da 2014.
Moses Aduku yace tawagar zata buga wasan farko da kasar Spain tamkar wasan karshe, “Muna fatan wasan da za mu yi da kasar Spain ya zama tamkar wasan karshe, Spain tawaga ce mai karfi amma ba za mu yi kasa a gwuiwa ba.”
Yanayin taka ledar Spain na baya-bayan nan ya nuna irin girman kalubalen da Nijeriya ke fuskanta, “La Roja” kamar yadda ake kiransu sun kai wasan karshe a gasar da aka buga kasar Faransa a shekarar 2018 kafin ta sha kashi a hannun Japan da ci 3-1 a wasan karshe, sai dai, ‘yar wasan gabansu, Patricia Guijarro ta lashe kyautar kwallon zinare da takalmin Zinare.
A shekarar 2010, Nijeriya ta kai wasan karshe a karon farko, inda ta doke Amurka a bugun fenariti a wasan kusa da na karshe da suka buga a birnin Augsburg na kasar Jamus kafin ta sha kashi a hannun Jamus mai masaukin baki da ci 2-0 a wasan karshe a birnin Bielefeld.














