An Zartas Da Sanarwar Chengdu A Taron Ministocin Kungiyar APEC Kan Harkar Raya Fasahohin Dijital Da AI
An kira taron ministocin kungiyar hadin gwiwa kan tattalin arziki ta nahiyar Asiya da tekun Pasific (APEC), kan harkar raya fasahohin dijital da kirkirarriyar basira ko AI na shekarar 2026, jiya Alhamis a birnin Chengdu na kasar Sin, inda aka zartas da sanarwar ministocin kungiyar APEC na shekarar 2026 game da ayyukan raya fasahohin dijital da AI, ko kuma sanarwar Chengdu a takaice. Cikin sanarwar, an cimma matsaya daya ta kafa kungiyar hadin gwiwar raya fasahohin digital da AI ta yankin Asiya da Pasifik, domin kafa tsarin zurfafa hadin gwiwa a fannin raya fasahohin tsakanin mambobin kungiyar APEC a nan gaba. Shugaban taron, kana ministan harkokin masana’antu da sadarwa na kasar Sin Li Lecheng ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da mambobin kungiyar ta APEC, ta hanyar amfani da tsarin kungiyar, da aiwatar da ra’ayi daya da aka cimma yayin taron na wannan karo, ta yadda za a zurfafa hadin gwiwa da mu’amalar dake tsakanin bangarori daban daban, don cimma moriyar bunkasuwar fasahohin dijital da AI, da kafa makoma mai haske cikin hadin gwiwa. (Mai Fassara: Maryam Yang)



















