Sin Na Ci Gaba Da Jan Zare A Fannin Bunkasa Hanyoyin Sufurin Jiragen Kasa Da Habbaka Tattalin Arziki
A duniyar da ke cike da dimbin al’umma, samarwa da inganta hanyoyin sufuri, ba wai alfarma ba ce, abu ne...
A duniyar da ke cike da dimbin al’umma, samarwa da inganta hanyoyin sufuri, ba wai alfarma ba ce, abu ne...
Kasar Sin ta bayyana cewa tana sa-ido sosai kan halin da ake ciki a yankunan Gabas ta Tsakiya, da Gulf,...
A yau Talata, shugaban kasar Sin, Xi Jinping, ya taya Luiz Inacio Lula da Silva murnar sake zabensa a matsayin...
A yau Litinin, 26 ga watan nan na Oktoba, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Guo Jiakun, ya bayyana a wani taron manema labarai cewa, fasahar kirkirarriyar basira ta AI wani sabon fanni ne mai kunno kai a cikin harkokin jagorancin duniya, kuma gwaji ne na tantance inganci ga tsarin jagorancin duniya. Tsarin jagorancin duniya yana bukatar kokari na gaske don karfafa wakilci da fada-a-jin kasashe masu tasowa. Guo ya bayyana cewa, kwanan nan a yayin taron dandalin inganta jagorancin duniya na shekarar 2026 (wanda aka gudanar a Xiongan), kasar Sin ta fitar da rahoton ci gaban da aka samu game da "Tsarin gina karfin fasahar AI don amfani da ita ta hanyar da ta dace kuma ga kowa da kowa." Abu na gaba kuma, kasar Sin na maraba da karin kasashe su shiga cikin Kungiyar Hadin Gwiwar Fasahar AI ta Duniya domin binciko karin hanyoyin hadin gwiwar kasa da kasa wajen gina karfin fasahar AI, tare da karfafa ci gaban fasahar AI a duniya domin amfani da ita ta hanyar da ta dace kuma ga kowa da kowa bisa daukar kwararan matakai. Dangane da takardar da kasar Sin ta fitar kwanan nan game da matsayin kasar kan inganta jagorancin harkokin sararin samaniya, Guo Jiakun ya bayyana cewa, wannan babban mataki ne da kasar Sin ta dauka domin aiwatar da abubuwan da ke kunshe a cikin manyan shawarwari na duniya guda hudu da ta gabatar, tare da zurfafa kokarin gina al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai-daya ga dan Adam a bangaren sararin samaniya. Kazalika, kasar Sin za ta ci gaba da aiki tare da dukkan bangarori bisa ruhin bude kofa da gina abubuwa masu ma’ana, domin tabbatar da cewa sakamakon ci gaban da aka samu a bangaren sararin samaniya ya zama mai amfanarwa ga daukacin bil’Adama. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Ranar 25 ga watan Oktoban nan, ita ce ta cika shekaru 55 da maido wa kasar Sin halastacciyar kujerarta a Majalisar Dinkin Duniya (MDD). A cikin wata makala mai taken "Daga Geneva zuwa shekaru 55 na alakar Sin da MDD" wadda aka rubuta domin wannan lokaci, Jia Guide, wakilin dindindin na kasar Sin a ofishin MDD da ke Geneva da sauran kungiyoyin kasa da kasa, ya bayyana cewa kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da dukkan bangarori domin karfafa rawar da MDD ke takawa, da kuma inganta tsarin mabambantan bangarori. Jia Guide ya ce, a matsayinta na mambar da aka kafa MDD da ita kuma mamba ta dindindin a kwamitin sulhu, Sin ta kasance a koyaushe tana goyon bayan ci gaba da bunkasa ginshikai uku na MDD, wato zaman lafiya da tsaro, ci gaba, da kuma kare hakkin dan Adam. A matsayinta na kasa daya tilo a duniya da ta rubuta kudurin bin hanyar samun ci gaba cikin lumana a cikin kundin tsarin mulkinta, Sin ta kasance a koyaushe tana bin manufar hulda da kasashen waje ta zaman lafiya mai zaman kanta kuma ta tura sama da sojojin kiyaye zaman lafiya 50,000, wanda hakan ya sanya ta zama babbar mai ba da gudummawar dakarun kiyaye zaman lafiya kuma ta biyu mafi bayar da gudummawar kudi ga ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD a tsakanin membobin dindindin na kwamitin sulhu. Jia Guide ya rubuta cewa, a 'yan shekarun baya-bayan nan, yayin da ake fuskantar muzgunawa daga bangare guda da kuma yanayi mai karo da juna, kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen kare manufofi da ka'idojin kundin tsarin MDD. Haka kuma, ta yi amfani da dandaloli da tsare-tsare daban-daban kamar na "Kungiyar Abokai kan Inganta Jagorancin Duniya" da ke Geneva da kuma "Ranar Tattaunawa a tsakanin Wayewar Kai Daban-daban ta Duniya", domin karfafa gwiwar al'ummar duniya wajen samar da cimma matsaya kan kiyaye tsarin mabambantan bangarori da kuma neman asalin ginshiki mafi girma da ya hade kowa da kowa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga ranar 23 zuwa 25 ga wata, kasashen Afrika 5 sun karbi bakuncin bikin nune-nunen hotuna, albarkacin cikar yankin Taiwan shekaru 81 da dawowa karkashin ikon mulkin kasar Sin. Kasashen 5 na Afrika sun hada da Kenya da Nijeriya da Afrika ta Kudu da Tanzania da kuma Mozambique. A shekarar 2025, kwamitin dindindin na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ya yanke shawarar ayyana ranar 25 ga watan Oktoba a matsayin ta tunawa da Dawowar Taiwan Babban Yankin Sin, da kokarin kare nasarorin yakin duniya na II da ma odar duniya bayan yakin. Me karbar bakuncin wadannan nune-nune da kasashen Afrika suka yi yake nufi? Amincewa da kiyaye manufar “kasar Sin daya tak a duniya,” da kasancewar Taiwan wani bangare na kasar da ba zai iya ballewa ba, ita ce tushen kulla dangantaka tsakanin Sin da daukacin kasashen duniya. Batun da ya shafi yankin Taiwan, batu ne mai muhimmanci ga kasar Sin, kuma batu ne na cikin gida. Don haka, ba shakka yadda kasashen Afrika suka karbi bakuncin nune-nune ya kara tabbatar da yadda suke girmama cikakken ’yancin Sin da iko kan yankunanta. Ya kara bayyana mana kyakkyawar alakar dake tsakanin bangarorin biyu, domin ya nuna cewa, yadda Sin ke tsaya musu a dandalin kasa da kasa da yadda take goyon bayan ci gabansu, su ma suna girmama burika da muradunta. Wannan ita ce abota ta kwarai da aminci bisa mutuntawa da girmama juna. Duk da cewa wasu kasashe na ingizawa tare da aikewa da mummunan sako ga masu neman ballewa da samun ’yancin kan Taiwan, kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen kare nasarorin da aka samu bayan yakin duniya na II. Cikin shekaru 81 da suka gabata, daya daga cikin nasarori mafiya muhimmanci ita ce, kokarin Sin na ci gaba da tabbatar da kasancewar Taiwan wani bangare na kasar, da kokarin tabbatar da dunkulewar kasar da ma son ganin ci gaban yankin, kamar yadda ya dace babbar kasa ta yi. Wannan kadai, ya isa nunawa masu neman ballewa da magoya bayansu cewa, hakarsu ba za ta taba cimma ruwa ba. Kuma yayin da tsarin duniya ya sauya, watau kai ya waye, kasashe masu tasowa suke samun ci gaba cikin sauri da kokarin dogaro da kansu (godiya ga kasar Sin), ba za su bari hannun agogo ya koma baya ba, za su hada hannu da Sin wajen samar da duniya mai daidaito da adalci da rarrabuwar iko tsakanin kasa da kasa. Kuma ba makawa za su bayar da gagarumar gudunmuwa wajen ganin dunkulewar dukkanin yankunan Sin wuri guda, maimakon ballewar wani yanki. (Fa’iza Mustapha)
An gabatar da nune-nunen hotuna, albarkacin cikar Taiwan shekaru 81 da dawowa karkashin ikon kasar Sin, a kasashe 5 na...
Tun bayan shiga sabuwar shekarar nan ta 2026, maaikatar cinikayya ta kasar Sin ta aiwatar da kudurori yadda ya kamata,...
Tun daga yau Litinin 26 zuwa Alhamis 29 ga watan nan na Oktoba, kwamitin tsakiya na 20 na jamiyyar kwaminis ta kasar Sin, zai gudanar da cikakken zama na biyar a birnin Beijing. Babbar ajandar taron na wannan karo ita ce: Hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS za ta gabatar da rahoton aiki na kwamitin tsakiya, da nazartar muhimman batutuwa masu nasaba da ci gaba da ingantawa da tsauraran matakan gudanar da mulki na jam'iyya daga dukkannin fannoni. (Saminu Alhassan)
A yayin da ake cika shekaru 81 da maido da Taiwan kasar Sin kuma cika shekara daya da kafa ranar maido da Taiwan kasar Sin, an gudanar da taron karawa juna sani na murnar cika shekaru 81 da maido da Taiwan kasar Sin a birnin Fuzhou dake lardin Fujian na kasar Sin a yau Lahadi 25 ga wannan wata. A gun taron, direktan ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta Sin kuma na majalisar gudanarwar kasar Sin, Song Tao, ya bayyana cewa, jam’iyyar kwaminis ta Sin da kuma gwamnatin kasar Sin sun kafa ranar maido da Taiwan kasar Sin don shaida imanin kasar Sin na tabbatar da ikon mallakar kasa da kiyaye martabar yankunan kasar, da kuma tsayawa tsayin daka kan manufar Sin daya tak a duniya. Ya kamata jama’ar gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan su bi tunanin yaki da hare-hare tare da raya al’ummar kasar, da kin amincewa da duk wani irin yunkurin ‘yan aware na yankin Taiwan da kuma tsoma baki daga waje kan batun. (Zainab Zhang)
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.