An Gabatar Da Littafin “Bayanan Xi Jinping Kan Basirar Gudanar Da Ayyuka A Kananan Hukumomi”
A kwanakin baya, an gabatar da littafin “Bayanan Xi Jinping kan basirar gudanar da ayyuka a kananan hukumomi” a dukkan...
A kwanakin baya, an gabatar da littafin “Bayanan Xi Jinping kan basirar gudanar da ayyuka a kananan hukumomi” a dukkan...
A lokacin zafi na bana, an samu karuwar zafi mai tsanani a kasashen nahiyar Turai, inda kuma kayayyakin Sin na magance zafi suka jawo hankalin jama’ar kasashen sosai, kamar su na'urar sanyaya wurare ta tafi da gidanka, da laima mai fesa ruwa don magance zafin rana, da fanka da ake iya daurawa a kugu da sauransu. Wata kididdiga ta nuna cewa, yawan na’urorin sanyaya iska da kasar Sin ta fitar zuwa kasashen yammacin Turai ciki har da Faransa, da Netherlands, da Belgium da sauransu, a watanni biyar na farkon bana, ya ninka har sau biyu bisa na makamancin lokaci na bara. A watan Yuni, yawan na’urorin da kasar Sin ta sayar ga nahiyar Turai, sun karu da kashi 72.8 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara. A baya, an jima sai an huda bangwayen tsoffin gine-ginen da aka yi a kasashen nahiyar Turai, idan ana son hada na’urorin samar da sanyi wanda hakan ke kara kudin da ake kashewa don sanyaya iska, baya ga bukatar bin wasu matakai da dama. Amma daga bisani kamfanonin Sin sun gano dabarar samar da na’urorin sanyaya iska na tafi da gidanka, wadanda ba sa bukatar huda bango don kafa su. Irin wadannan na’urori na bukatar minti 10 kacal wajen hada su, da ajiye su inda ake bukata. Kayayyakin laturoni na kasar Sin suna biyan bukatun jama’ar kasashen Turai a fannin magance zafin rana a tsawon lokaci ta hanyoyin rike damar da suke da ita, da ingancinsu, da kuma hanzarin kai su wuraren da ake bukata. A halin yanzu, ana fuskantar ra’ayin killace kai daga wasu bangarori, da na bayar da kariyar cinikayya, kuma kungiyar EU ta gabatar da jerin matakan kayyade ciniki tsakaninta da kasar Sin tun daga farkon shekarar nan. Amma duk da wannan yanayi, an sayar da kayayyakin laturoni na Sin na magance zafi masu tarin yawa a sassan Turai, inda yawan kudin cinikayya a tsakanin Sin da EU a fannin, cikin watanni 5 na farkon bana ya karu da kashi 10.3 cikin dari, bisa na makamancin lokaci na bara, wanda ya shaida cewa, tushen hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Turai shi ne samun moriyar juna. Kasar Sin tana kokarin samar da sabbin gudummawarta, wajen sa kaimi ga samun ci gaba tare a sauran sassan duniya. Lamarin da ya shaida cewa, kasar Sin abokiyar hadin gwiwa ce, kuma za ta ci gaba da samar da gudummawa ga ci gaban duniya baki daya. (Zainab Zhang)
Rundunonin sojojin ruwan kasar Sin da na Rasha sun shirya gudanar da atisayen soji, da sintiri na hadin gwiwa a...
An kaddamar da cibiyar horar da ma’aikatan jinya ta kasashen Sin da Saliyo, a asibitin sada zumunta na Saliyo da...
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce Sin ta sha alwashin karfafa musaya da kasar Sweden a dukkanin fannoni, da amfani da fifikonsu, da ingiza hadin gwiwar cimma moriyar juna, da bunkasa dangantakarsu bisa turba mai nagarta, daidaito da dorewa. Wang Yi, ya bayyana hakan ne a jiya Asabar, yayin da yake zantawa da firaministan Sweden Ulf Kristersson a birnin Stockholm. Wang, ya kuma ce alakar Sin da Sweden ta gamu da wasu wahalhalu a shekarun baya-bayan nan, kuma wani abu mai matukar muhimmaci ga sassan biyu shi ne karfafa shawarwari, da bunkasa fahimtar juna, da gina aminci, tare da kara fahimtar juna yadda ya kamata. Kazalika, karuwar ci gaban kasar Sin zai amfani duniya baki daya, tare da samar da sabbin damammaki ga dukkanin kasashen duniya, ciki har da Sweden. Wang ya kuma yi fatan Sweden za ta taka muhimmiyar rawa wajen kyautata alakar Sin da Turai. A nasa bangare kuwa, mista Kristersson ya ce gwamnatin Sweden na nacewa manufar kasar Sin daya tak a duniya, kuma a shirye take ta karfafa tattaunawa, da fadada amincewa juna, da ingiza hadin gwiwar cimma moriya mai kyakkyawar makoma a dukkanin fannoni tare da Sin. Ya ce Sweden na goyon bayan Turai da Sin a fannin karfafa shawarwari, da inganta shawo kan sabanin dake tsakaninsu. (Saminu Alhassan)
Rundunar dakarun tsaron teku ta Sin ko CCG, na ci gaba da sintirin wanzar da doka a sassan yankunan ruwa...
Kwanan nan wasu matasa sama da 20 daga jihar Washington ta kasar Amurka, sun ziyarci lardin Sichuan na kasar Sin,...
An yi bikin baje kolin tsarin samar da kayayyaki na duniya na Sin karo na 4, wato CISCE a takaice,...
Tawaga ta biyu ta kwararrun jami’an lafiya daga kasar Sin, ta sauka a birnin Kinshasa na janhuriyar dimokaradiyyar Congo a...
A madadin kasar Sin mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin He Wei, ya ziyarci birnin Tehran na...
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.