Tawaga ta biyu ta kwararrun jami’an lafiya daga kasar Sin, ta sauka a birnin Kinshasa na janhuriyar dimokaradiyyar Congo a jiya Juma’a, domin shiga ayyukan hadin gwiwar kasa da kasa na karfafa kandagarki da shawo kan cutar Ebola. Jami’i a ma’aikatar lafiyar kasar Luku Maleyo Marius ne ya tarbi tawagar a filin jirgin saman kasar.
Da yake tsokaci bayan isar jami’an, shugaban tawagar kwararrun Gu Zhiqiang, ya ce za su fara aiki nan da nan, da hadin gwiwar kut da kut da cibiyoyin kiwon lafiya na Congo. Kuma za su samar da tallafin kwarewa ta fuskar binciken yaduwar kwayoyin cututtuka, da gwaje-gwaje a dakunan bincike, da jinyar marasa lafiya, da kandagarki da shawo kan cutar, da ma horar da jami’ai, da gabatar da kwarewar kasar Sin cikin ayyukan kyautata kandagarkin bazuwar cutar a Congo, da shawo kan ta, da karfin ikon samar da jinya.
A ranar Alhamis, shugaban janhuriyar dimokaradiyyar Congo Felix Tshisekedi, ya bayyana godiya ga kasashe kawayen kasarsa, da ma hukumomin kasa da kasa ciki har da Sin, bisa goyon bayan da suke baiwa kasarsa a yakin da take yi da cutar Ebola. (Saminu Alhassan)













